✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jini ta hanci ta baki ya rika zuba bayan yi wa wata mata rigakafin Coronavirus a Kaduna

Ta kwanta jinya a Asibitin ne bayan kwanaki shida da yi mata rigakafin.

Wata mata mazauniya a Jihar Kaduna mai suna Hannatu Tanko, ta bayar da labarin yadda ta rika zubar jini ta hanci da baki bayan karbar allurar rigakafin Coronavirus.

Matar ta bayyana lamarin ne a wani hoton bidiyo da ya karade shafukan intanet, wanda ya nuna an yi mata allurar ne a wani Asibitin Kwararru na Ashmed da ke birnin Kaduna.

Kodayake, matar ta ce an yi mata rigakafin ne a wata Sakateriya a Kudancin Kaduna, amma mutane da dama sun alakanta ta da asibitin na Ashmed.

Domin nesanta kansu daga wannan rudani, Babban Likitan Asitin na Ashmed, Dokta Patrick Echobu, ya jawabi a wani taron manema labarai a ranar Alhamis.

A cewarsa, matar ta kwanta jinya a Asibitin ne bayan kwanaki shida da yi mata rigakafin a wani wurin na daban.

Dokta Echobu ya ce, “A madadin Asibitin Ashmed, muna so mu nesanta kanmu tare da yin Allah wadai da bidiyon da ake yadawa kan daya daga cikin majiyatanmu, wacce ta kawo kanta ranar 30 ga watan Maris tana fama da zubar jini daga baki da hancinta.”

“Mun karbe ta a matsayin mara lafiya ba tare da sanin cewa ta yi allurar rigakafin kwana shida da suka gabata a wani wurin na daban sannan ta bai wa wani dama ya dauki hotonta har aka rika yada wa a yanar gizo.”

“Ba wai muna cewa ba mu da alaka da labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta ba, amma muna so kowa ya sani cewa dukkanin ma’aikatan Asibitin Ashmed an yi musu allurar rigakafin.”

Dokta Echobu ya ci gaba da cewa, akwai yiwuwar amai na jini ta hanci da baki da matar ta rika yi yana da nasaba da wasu cututtukan da take fama da su kamar hawan jini, da wasu cututtukan da suka shafi kafofin shakar iska da numfashi.

Sai dai ya ce sun samu nasarar shawo kan matsalar zubar jinin bayan an kwantar da ita a asibitinsu.

Ya ce tawagar wasu kwararrun likitoci daga Ma’aikatar Lafiya sun ziyarci matar domin tabbatar yanayin koshin lafiyarta.

Dangane da amincin rigakafin, Dokta Echobu ya bayar da tabbacinsa a kanta tare da yaba wa Gwamnati a bisa kokarin da ta yin a samar da rigakafin ga al’umma.

Ana dai ci gaba da cece-kuce a kan amincin rigakafin Astraznene wacce ake ci gaba da yi wa al’umma allurarta a Najeria bayan wasu alamomi na rashin karbar jiki ko jini da ta yi wa wasu sun bayyana.

Fiye da kasashen nahiyyar Turai goma ne suka dakatar da yi wa al’ummominsu rigakafin, amma daga bisani bayan Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da ingancinta aka ci gaba.