✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun hallaka ‘yan bindiga 100 a Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kai wani mummunan hari ta jiragenta wanda ya hallaka akalla ’yan bindiga 100 tare da tarwatsa sansanoninsu kusan…

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kai wani mummunan hari ta jiragenta wanda ya hallaka akalla ’yan bindiga 100 tare da tarwatsa sansanoninsu kusan bakwai a Jihar Zamfara.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ’yan bindigar suke kaiwa ke kara kamari a jihar.

Daraktan watsa labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola wanda ya tabbar da hakan a ranar Juma’a ya kuma ce an kai harin ne da nufin tarwatsa sansanonin bata-garin domin samar da aminci a jihar.

Daramola ya ce rundunar tsaro ta musamman a yankin da ake wa lakabi da Operation Hadarin Daji ce ta kai hari da ta yi wa lakabi da ‘OPERATION WUTAR DAJI 2.

A cewarsa, an kai harin ne a dazukan Damboru, Kuyambana, Dutsen Asola da kuma Dutsen Bagai.

Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar wanda yanzu haka yake yankin, ya ce suna samun nasarori a farmakin da suke kai wa sansanonin ’yan bindigar a jihar ta Zamfara.

Abubakar ya ce suna amfani da na’urori da ke gano maboyar ’yan ta da kayar bayan, wanda hakan ya ba su damar wargaza su.

Jihar Zamfara ta jima tana fama da matsalolin tsaro a ’yan shekarun nan da suka hada da hare-haren ’yan bindiga, barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.