✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun halaka mayakan ISIS a Najeriya

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yi galaba a wani farmaki da ta kai kan mayakan kungiyar ISIS a maboyarsu da ke Bukar Meram daf…

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yi galaba a wani farmaki da ta kai kan mayakan kungiyar ISIS a maboyarsu da ke Bukar Meram daf da Gabar Tabkin Chadi a Jihar Borno.

Sojojin Rundunar Operation Lafiya Dole, sun kashe kwamandojin mayakan na ISIS gami da tarwatsa sansaninsu a yankin da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Cikin sanarwar da ya fitar, Jami’in Hulda da Jama’a Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ce sojojin sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama a Dole, wata alkarya a Kudancin Jihar Borno.

Ya ce sojojin sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai harin a ranar 17 ga watan Agusta, bayan tattaro bayanan sirri da leken asiri da suka gudanar.