✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun hallaka daruruwan ’yan bindiga a Sakkwato

An yi wa maharan ruwan bama-bamai yayin da suke kan hanyarsu bayan kai farmaki wasu yankuna.

Wasu jiragen yakin sojoji sun kashe ’yan bindiga masu yawan gaske a kauyen Rarah da ke Karamar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato.

An shafe shekaru ana kai hare-hare a Karamar Hukumar Rabah da ke gabashin Jihar Sakkwato.

Yankin dai ya yi iyaka da Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

A cewar dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Abdullahi Zakari, sojoji sun kai harin bama-bamai a wurare uku, wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan ‘yan bindiga.

Ya ce ‘yan bindigar na dawowa ne daga hare-haren da suka kai a lokacin da aka kashe su.

“Sun kai hari kusan kauyuka 17, sun kashe mutane uku tare da yin awon gaba da dabbobi da dama,” in ji shi.

Zakari ya bayyana harin da sojojin suka kai a matsayin wanda aka fi samun nasara a ‘yan kwanakin nan.

“Yadda sojojin suka amsa kiran da muka yi suka duba damuwarmu har ma suka hada jiragen yakinsu, wannan abin a yaba ne matuka.

“Muna fatan za su ci gaba da hakan saboda ‘yan bindiga sun shafe shekaru suna ta’addanci ga mutanenmu ba tare da kawo mana dauki ba,” in ji shi.

Binciken da aka yi ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan Kware da Rabah kafin daga bisani sojoji suka yi musu ruwan bama-bamai a kauyen Rarah.

Wani mazaunin Rarah, Ibrahim Rarah, ya ce sun kirga gawarwakin maharan sama da 16 a daya daga cikin yankunan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya ce ba a sanar da shi faruwar lamarin a hukumance ba, inda ya yi alkawarin yin cikakken bayani da zarar ya samu bayanin abin da ya faru.