✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun yi wa Boko Haram ruwan wuta a Borno

’Yan ta’adda da dama sun mutu a luguden wutar jiragen yakin

Dakarun Sojin Saman Najeriya karkarshin Rundunar Operation  Lafiya Dole sun yi ruwan wuta da jiragen yaki a kan mayakan Boko Haram a yankin Mainok, Jihar Borno.

Kakarin Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo-Janar John Enenche ya sanar da haka yayin karin haske kan ayyukan soji na murkushe Boko Haram, a ranar Labara

Enenche ya ce jiragen yakin sun yi wa mayakan Boko Haram din luguden wuta ne a lokacin da jerrin gwanon motocin yakin kungiyar ke kai-komo kan hanyar Jakana zuwa Mainok.

Ya ce nan take jiragen yakin suka yi ta barin wuta a kan ayarin motocin na Boko Harm da suka hada da wasu motocin dakon kaya.

Enenche ya ce “luguden wutan ya hallaka da dama daga cikin ’yan ta’addar,” yayin da motocin nasu suka rika ci da wuta suka kone kurmus.