✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen yaki sun yi wa ’yan bindiga luguduen wuta a Sakkwato da Katsina

An kashe da dama daga cikin maharan da ke boye a dazukan.

Jiragen Sojin Saman Najeriya sun yi nasarar hallaka ’yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu a dazukan jihohin Sakkwato da Katsina.

A daya daga cikin hare-haren, jiragen yakin sun lalata sansanin wani dan ta’adda da ake kira ‘Gajere’ inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma sun samu raunukan harbi.

A Jihar Sakkwato dakarun sojin karkashin rundunar ‘Hadarin Daji’ sun kai hare-hare ne ta sama a dazukan Mashema, Yanfako, Gebe da kuma Gatawa a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni.

Wata majiya ta soji  ta bayyana cewa an samu nasarar hakan ne a ruwan bama-bamai da suka yi ranar 5 ga watan Oktoba 2021, bayan sintirin da aka yi ta yi ta sama wanda ya gano wuraren da ’yan bindigar ke boyewa a cikin dazukan.

Rahotanni sun ruwaito mutanen da ke zaune a yankunan da aka kai hare-haren suna bayar da labarin yadda suka ga maharan na ta tserewa, yayin da wasu suka fake a wata makarantar firamare da ke kauyen Bafarawa.

A Jihar Katsina an gano yadda jiragen yakin Najeriya suka yi ta ruwan bama-bamai a maboyar maharan a dajin Rugu da ke da iyaka da Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina a tsakanin ranar 30 ga watan Satumba da 3 ga watan Oktoba, 2021.