✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgi dauke da mutum 62 ya yi batan dabo a Indonesia

An nemi wani jirgin fasinja mai dauke da mutum 62 an rasa bayan tashinsa daga Jakarta, babban birnin kasar Indonesia a ranar Asabar. Shafin da…

An nemi wani jirgin fasinja mai dauke da mutum 62 an rasa bayan tashinsa daga Jakarta, babban birnin kasar Indonesia a ranar Asabar.

Shafin da ke bin diddigin jiragen sama na Flightradar24.com ya ce jirgin ya yi batan dabo ne bayan ya yi tafiyar akalla kafa 10,000 cikin kankanin lokaci dai bai wuce minti daya ba yayin da yake gangarowa kasa.

Hukumomi sun bayyana cewa jirgin na Boeing 737 mallakar Kamfanin Sriwijaya Air ya yi batan dabo yayin da yake kan hanyar zuwa yankin Yammacin Kalimantan.

Kamfanin zirga-zirga na cikin gida na Sriwijaya Air ya ce yana ci gaba da tattara bayanai game da jirgin a yayin da Ma’aikatar Sufurin Kasar Indonesia ta tabbatar da yunkurin da ta afka ciki domi aikin ceto.

Adita Irawati, mai magana da yawun Ma’aikatar Sufurin kasar ta ce jirgin mai dauke da fasinja 56 da ma’aikata 6 wanda ya tashi da misalin karfe 1 da minti 56, an daina jin duriyarsa ne da misalin karfe 2.40 na tsakar rana.