✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin da ya yi saukar gaggawa a Banki ya isa Maiduguri

Rundunar Sojin Sama ta karyata labarin cewa Boko Haram ta harbo helikwafta a Jihar Borno

Helkiwaftan da ya yi saukar gaggawa a garin Banki, Jihar Borno ya isa Maiduguri bayan an yi masa gyara.

Da farko wata majiyar da masu aikin jinkai ya ba mu rahoton da ke cewa ana fargabar mayakan Boko Haram ne suka harbo jirgin da ke dauke da fasinjoji a Karamar Hukumar Bama.

Helikwaftan agaji na Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) ya yi saukar gaggawa ne jim kadan bayan tashinsa daga Banki zuwa Maiduguri.

Bayan saukar gaggawar, sojoji sun hanzarta kai wa ayarin dauki yayin da suka yi masa gyaran gaggawa kafin komawar Maiduguri daga baya.

Rundunar sojin Sama ta Najeriya ta ce, “babu wani helikwafta da aka harbo ko ya fado a Jihar Borno a yau [Talata]; amma tabbas jirgin Majalisar Dinkin Duniya ya je aiki Banki kuma tuni ya dawo Maiduguri”.

Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce, “ya kamata Daily Trust [mamallakin Aminiya] su tuntubi hukumomin da abin ya shafa kafin su wallafa labarin”.