✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin farko dauke da Alhazan Kwara 541 ya iso Najeriya

Alhazan su 541 dai sun sauka ne a Ilorin

Rukuni na farko na Mahajjata 541 na  jihar Kwara sun dawo gida Najeriya a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa jirgin na kamfanin Max mai lamba 5N-ADM da ya dakko mahajjatan ya sauka a filin jirgin saman Ilorin, babban birnin Jihar ta Kwara, da misalin karfe 8:00 na safe.

Mahajjatan sun sauka lafiya inda suka koma ga iyalai da ’yan uwa da suka kwana a filin jirgin domin tarbar su.

Wasu daga cikinsu sun bayyan godiyarsu ga Allah kan ba su damar sauke faralin, tare da mika godiya ga gwamnatin jihar Kwaran bisa yadda ta yi dawainiya da su a kasa mai tsarkin.

Wani Alhaji mai suna Tunde Kanike ya ce Gwamnati ta yi kokari wajen ganin sun sauke faralin cikin nasara, tare da jan hankalin ta kan inganta bangaren walwalar al`ummnar ta.

“Ya kamata Hukumar Kula da aikin Hajji ta jihar mu ta kara kokari wajen samar mana abincinmu na gida a kasa mai tsarki, hakan zai taimaka mana sosai a gaba”.

Ita ma wata Hajiyar Kuburat Abimbola Lawal ta bada makamnaciyar waccan shawarar ta Tunde, tare da mika godiyarta ga Allah bisa ba ta ikon sauke faralin na bana.

Mahajjata dubu 1,409 ne dai har da ma`aikatan Hukumar kula da aikin Hajjin jihar suka samu sauke faralin na bana daga Kwaran.