Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya | Aminiya

Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya

Wasu maniyyata Aikin Hajji
Wasu maniyyata Aikin Hajji
    Rabilu Abubakar, Gombe

Jirgin farko dauke da mainiyyatan Jihar Gombe su 508 ya tashi daga filin jiragen sama na kasa da kasa da ke garin Lawanti a Jihar Gombe zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Ana sa ran jirgin kai tsaye zai wuce filin jirgin saman Sarki Abdulazeez da ke Jidda a kasar ta Saudiyya.

Maniyatan ana sa ran daga birnin na Jiddah za su wuce zuwa birnin Madina don gudanar da ziyarya a Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W.)

Jirgin na kamfanin Max Air ya tashi ne a ranar Lahadi.

Mahajjatan za su yi kwanaki biyar ne a Madina kafin su wuce zuwa birnin Makka kafin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan

Ana sa ran jirgi na biyu zai tashi da wani rukunin maniyyatan a ranar Litinin mai zuwa.