✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin karshe ya tashi ya bar shugaban hukumar alhazan Kano da wasu maniyyata 745 a kasa

Hakan ta faru duk da kara wa'adin da aka yi ta yi

Jirgin karshe ya bar shugaban Hukumar Jin-dadin Alhazai na Jihar Kano, Abba Danbatta, wasu Daraktocin hukumar da wasu maniyyata 745 a kasa, inda ba za su sami damar sauke farali ba a bana.

Jirgin na kamfanin Azman, wanda ya tashi wajen misalin karfe 3:40 na yammacin Alhamis, ya bar maniyyatan ne duk da karin wa’adin da kasar Saudiyya ta yi wa Najeriya.

Da yake zantawa da manema labarai a safiyar Alhamis afin tashin jirgin, Sakataren Zartarwa na Hukumar Alhazai ta jihar Kano, Abba Danbatta, ya ce lamarin ya yi matukar sanya shi bakin ciki ganin yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta gaza cika alkawarin taimakawa wajen kwashe ragowar maniyyatan na Kano.

Danbatta ya ce, “A yau [Alhamis], jirgin Azman mai daukar fasinjoji 400 zai tashi daga Kano dauke da maniyyata 250 kacal, inda ya bar sama da maniyyata tare da jami’an hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano.

Hukumar NAHCON dai ta yi alkawarin turo kamfanin jirgin FlyNas tun kwanaki biyu da suka gabata don taimakawa wajen karasa kwashe maniyatan Jihar, amma har yanzu ba hakan ba ta tabbata ba.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya kara da Kamfanin jirgin saman Azman ya yi jigilar maniyyata sau shida da mahajjata 1,175 sakamakon amfani da suke da kananan jiragen da ba su da karfin daukar maniyata masu yawa.

Danbatta ya kara da cewa wannan ne ya sa suka koka kafin a fara jigilar maniyyatan aikin Hajji ganin cewa suna da mafi yawan alhazai, kuma sun yi bayanin cewa sun fi son jirgin kamfanin Max Air ya dauki maniyatan Jihar saboda yawan da suke da su.

Sakataren zartarwar ya kara da cewa ya je hedkwatar hukumar NAHCON da ke Abuja sama da sau 10 a a kan wannan batu, sannan ya rubuta wa hukumar wasiku sama da 11 don kada a shiga cikin wannan hali kuma shi ma Gwamnan Kano da kansa sai da ya rubuta musu wasika har sau uku, amma abin da ake gudu sai da ya faru.