✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasa ya kashe mutum daya a Makkah

An samu mutum guda da ya rasa ransa sakamakon wani hatsarin jirgin kasa da ya auku a kusa da birnin Makkah na Kasar Saudiyya. Kafar…

An samu mutum guda da ya rasa ransa sakamakon wani hatsarin jirgin kasa da ya auku a kusa da birnin Makkah na Kasar Saudiyya.

Kafar Talabijin ta Arabiya ta ruwaito cewa, jirgin wanda mallakin Kamfanin Saudiyya da Spain SSTPC, ya yi taho mu gama ne tsakanin nisan kilomita 4 da tasharsa a garin Makkah.

Bayanai sun ce hatsarin ya rutsa da mutumin da aka kashe ne yayin da yake tafiya kan titin jirgin.

Hukumomi sun yi kira ga mutane su rika nesa-nesa da titin jirgin kasa.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa,a shekarar 2018 ce aka kaddamar da jirgin mai gudaun tsiya domin jigila daga Makkah zuwa Madina, biranen da Masallatai mafi daraja ga muslumi suke a kasar.

Jirgin na Haramain Train shi ne mafi girman aikin sufuri da aka kaddamar baya bayan nan a kasar.