✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasa ya yi hatsari a Kano

An yi gaggawar garzaya wa da mutane da dama zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad a Kano.

An samu wani hatsarin jirgin kasa da ya wancakalar wata Tirela da ta dauko siminiti a Jihar Kano.

Bayanai sun ce hatsarin wanda ya rutsa da wani babur mai kafa uku da aka fi sani da A daidaita Sahu ya auku ne a kan titin Obasanjo da ke kwaryar birnin Dabo a ranar Lahadi.

Wasu ganau da ke gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kusa da digar jirgin, sun bayar da shaidar cewa sun hango tirelar a lokacin da ta tunkaro layin dogon a yayin da jirgin kasa shi kuma ya taho a sukwane.

Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, mashaidan sun ce sun yi kokarin ankarar da direban tirelar amma bai lura ba wanda a dalilin haka mai aukuwar ta auku.

A yayin da dai babu tabbacin ko an samu asarar rai a sakamakon hatsarin da ya auku, sai dai an yi gaggawar garzaya wa da mutane da dama zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.