✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya lalace a daji

Fasinjoji da dama sun bayyana damuwarsu kan lalacewar jirgin.

Daruruwan fasinjoji da suka taso daga Kaduna zuwa Abuja jirgin kasa sun shiga halin rashin tabbas bayan lalacewar jirgin a daji.

Aminiya ta ruwaito cewa jirgin ya sami matsala ne minti biyar bayan tashinsa daga tashar Rigasa a Kaduna; Sau yake tsayawa a hanya, kafin ya isa tashar kauyen Dutse, inda daga karshe ya lalace baki daya.

Sau biyu dai jirgin yana tsayawa a hanya kafin ya isa tashar kauyen Dutse, inda daga karshe ya lalace baki daya.

Daya daga cikin fasinjojin jirgin, kuma Mataimakin Sakataren Kungiyar  ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Midat ​​Joseph, ya ce jirgin ya samu matsala ne da misalin karfe bakwai na safe.

“Na bar gidana tun da karfe 5 na safe don shiga jirgin karfe 6:40 na safe, amma abin takaici jirgin ya lalace.  Wannan ba shi ne karo na farko da na taba fuskantar wannan matsalar ba,” inji shi.

Kazalika, wani fasinjan jirgain ya bayyana yadda shi ma ya fuskanci irin wannan matsalar a baya, inda ya shafe sa’a shida kafin ya isa Abuja.

“Wannan abin takaici ne. A ranar Asabar, mun kwashe sa’a biyar daga Abuja zuwa Kaduna. Mun bar Abuja karfe shida na yamma, amma ba mu isa Kaduna ba sai 11 na dare,” a cewar fasinjan.

Wani injiniyan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) wanda ya yi wa fasinjojin jawabi ya shaida musu cewa aikin gyaran jirgin zai dauke su kimanin sa’o’i biyu kafin a iya kammala shi.

“Muna takaicin lalacewar jirgin. Mun tuntubi tashar jirgin kasa ta Idu don kawo wani jirgin da zai dauke su zuwa Abuja,” inji jami’in.