✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin ruwa makare da tan 750 na man Diesel ya nitse a Tunisiya

Ana dai zargin rashin kyawun yanayi ne musabbabin hatsarin

Hukumomin kasar Tunisiya sun tabbatar da nitsewar wani jirgin ruwan dakon mai da ke makare da tan 750 na man Dizal a gabar kogin Gabes da ke Kudu maso Gabashin kasar.

Ana dai alakanta musabbabin hatsarin jirgin da rashin kyawun yanayi, yayin da hukumomi ke kokarin kauce wa abin da suka kira annoba ga muhalli.

Tuni dai aka kafa shingaye tare da yi wa jirgin kawanya, kamar yadda Ma’aikatar Muhallin Kasar ta tabbatar.

Rundunar Sojin Ruwan Kasar dai ta ce dakarunta sun samu nasarar ceto dukkan direbobin jirgin su bakwai a raye.

Ministar Muhallin Tunisiya, Leila Chikhaoui, wacce ta je har gabar ruwan ranar Asabar don ganewa idanunta aikin ceton da ke gudana, ta ce yanzu komai na karkashin kulawa.

“Muna kyautata zaton har yanzu jirgin bai huje ba, muna tunanin hakan zai taimaka mana wajen takaita illar hatsarin,” inji Ministar.

Leila ta kuma ce idan hali ya yi su nemi taimakon kasashen waje, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yin hakan.

Ta ce har yanzu suna jiran yanayi ya dada inganta kafin su aike da karin masu iyo don sake duba lafiyar jirgin.

Daga cikin matukan jirgin dai akwai dan kasar Georgia da mutum hudu ’yan Turkiyya da kuma mutum biyu ’yan Azerbaijan, wadanda aka garzaya da su asibiti, yanzu kuma suna otal suna hutawa.