✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin sama dauke da fasinjoji ya bace

Wan jirgin sama dauke da fasinjoji ya bace bat a sararin samaniya  kasar Costa Rica.

Wan jirgin sama dauke da fasinjoji ya bace bat a sararin samaniya  kasar Costa Rica.

Jirgin wanda ke dauke mutum biyar ’yan kasar Jamus daga Meziko ya bace ne da karfe 12.00 na dare (aggogon GMT) kafin wayewar garin Asabar, a cewar Ma’aikatar Tsaro ta Costa Rica.

Ministan Tsaron Costa Rica, Jorge Torres, ya ce, “Mun samu rahoton bacewar wani jirgi mai zaman kansa da ya taso daga Meziko zuwa filin jirgin,’ da ka yankin Lardin Limon da ke Gabashin Costa Rica.

Ministan tsaron ya ci gaba da cewa, “Jirgin yana dauke da Jamuwasa biyar,” a lokacin da ya bace.

Ya ce, “Sadarwa da shi ya katse ne daga kusa da turken sadarwa da ke La Barra de Parismina a Costa Rican Caribbean kuma nan take muka dauki matakan da suka dace” domin gano inda jirgin ya shige.

Sai dai ya bayyana cewa rashin kyan yanayi ya sa an dakatar da aikin neman jirgin, amma za a ci gaba daga safiyar Asabar.