Jirgin sama dauke da fasinjoji ya kama da wuta a Amurka | Aminiya

Jirgin sama dauke da fasinjoji ya kama da wuta a Amurka

    Sani Ibrahim Paki

Akalla mutum uku ne aka kwantar a asibiti bayan wani jirgin saman fasinjoji ya kama da wuta jim kadan da saukar shi a filin jirgin saman birnin Miami na Amurka ranar Talata.

A cewar hukumar kashe gobara ta birnin, jirgin na dauke ne da fasinjoji 126, sai ma’aikatan jirgi 11, lokacin da hatsarin ya auku.

Wani bidiyo ya nuna fasinjoji na ihun neman taimako lokacin da suke rige-rigen fita daga cikinsa.

Kafar yada labarai ta WSVN ta ba da rahoton cewa jirgin mallakin kamfanin sufurin jirage na Red Air ne kuma ya taso ne daga Jamhuriyar Dominica.

Ya taba kasa ne wajen misalin karfe 5:30 na yammacin Talata, sannan ya je ya doki wane gini a filin jirgin, kafin daga bisani ya tsaya a wani waje mai ciyayi a gefen wajen da jiragen ke gudu.