✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin saman Najeriya zai soma jigila a Afrilun badi — Hadi Sirika

Kamfanin zai samar da ayyukan yi kusan 70,000 ga ’yan Najeriya.

Ma’aikatar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya ta sanar da cewa zuwa watan Afrilun badi ake sa ran jirgin saman kasar zai fara aiki.

Ministan Ma’aikatar, Hadi Sirika ne ya tabbatar da hakan a tattaunarwarsa da manema labarai bayan zaman Majalisar Zartarwa da Shugban Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.

A cewarsa, kamfanin Jirgin kasar wanda Gwamnatin Tarayya ce za ta dauki nauyin kulawarsa da kaso 5 cikin 100, ’yan kasuwa a kasar za su rike kashi 46 cikin 100, yayin da ragowar kashi 49 ciki 100 zai kasance a karkashin wasu abokanan hulda da hadin gwiwa da kawo yanzu ba a mika musu ragamar ba ciki har da masu zuba hannun jari daga ketare.

Ministan ya ce an cimma matsayar kaddamar da kamfanin jirgin saman na Najeriya ne bayan jinkirin da aka rika samu wanda kusan sau biyar ana dakatar da shirin kafa kamfanin sufurin jrgin sama na gwamnatin kasar.

Sirika ya ce idan kamfanin ya fara aiki, zai samar da ayyukan yi kusan 70,000 ga ’yan Najeriya.

Aminiya ta ruwaito cewa, batun farfado da kamfani jirgin saman na Najeriya na hadin gwiwa ne da ’yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar kawai da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa

Ana iya tuna cewa, a watan Yulin 2018 ne gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da suna da kuma tambari ko alamar sabon kamfanin sufurin jirgin saman nata a lokacin bikin baje koli na Farnborough Airshow a Landan.

Bayanai sun ce da can baya Najeriya tana da kamfanin Nigeria Airways da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma’aikata.