✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin soji ya yi hatsari a kasar Masar

Helikwaftan soji ya rikito a yankin Sinai na kasar Masar.

Wani jirgin soji ya yi hatsari a kasar Masar inda ya kashe mutu bakwai da ake cikinsa.

Helikwaftan ya rikito ne a yankin Sinai na kasar Masar a lokacin da yake dauke da sojoji da masu aikin sa ido na hadin gwiwa.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce wadanda suka mutun sun hada da Amurkawa biyar, Bafaranshe daya da kuma dan Jamhuriyar Czech.

Wata majiya a Isra’ila ta ce jami’an da hatsarin ya ritsa da na daga cikin rundunar wanzar da zaman lafiya da aka kafa tun a 1979.

Ta ce an kafa rundunar ce a lokacin da aka kulla yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Masar kuma ba ta da alaka da Majalisar Dinkin Duniya.