✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin yaki ya kashe kasurgumin dan bindiga Alhaji Shanono da yaransa 18

An kashe kasurgumin dan bindiga, Alhaji Shanono da wasu yaransa 18.

Jiragen yakin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi Jihar Kaduna, mai suna Alhaji Shanono, tare da wasu yaransa 18.

Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Oladaya Amao, ya sanar a safiyar Alhamis cewa bayan kashe Alhaji Shanono da yaransa, an lalata bindigogi sama da 30 da babura 20 a harin.

Ya yi alkawarin cewa dakarunsa ba za su gajiya ba har sai sun kawar da ’yan bindiga da ke addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a Najeriya.

Sanarwa da Daraktan Yada Labarai na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ta umarci sojojin da su kara kaimi wajen kai samame da dabarun yaki.

A cewarsa, hare-haren da jiragen yaki suka kai a yankin Arewa maso Yamma a baya-bayan nan ya nuna cewa an kawar da ’yan ta’adda da dama tare da lalata matsugunansu.

Daga cikin bata-garin da aka aika lahira har da Alhaji Shanono da wasu yaransa 18, aka lalata bindigogi sama da 30 da babura 20.

Kazalika, ya ce an kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Gabas tare da taimakon rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai, inda jiragen yaki suka kai farmaki kan Boko Haram a Gazuwa, da ke Jihar Borno a ranar Asabar.

Babban Hafsan Sojin Saman ya gargadi kwamandojinsa da su sake jajircewa kan aikin da ke gabansu, na ganin an dawo da zaman lafiya kasar nan.