✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan jirgin ruwan fasinja

Fasinjoji da dama sun jikkata a jirgin ruwan da ya dauko kayan abinci.

Mutane da dama sun jikkata bayan wani jirin soji ya yi luguden wuta kan wani jirgin ruwan fasinja da ke dauke da kayan abinci a kan teku.

Ganau sun ce wani jirgin yaki da ake zargin na sojoji ne ya bude wuta ne a lokacin da jirgin ruwan ke hanyarsa ta zuwa tsibirin Bonny Islanda daga Fatakwal, Jihar Ribas.

“Jirgin dakon kayan na dauke da garin rogo da shinkafa da sauran kayan abinci daga Fakwal zuwa Bonny.

“Yana kaiwa Okrika Dutch Island a hanyarsa ta zuwa Bonny, wani jirgin yaki da ake zargin na sojoji ne ya bude masa wuta, mutane da dama daga cikin fasinjojin da jirgin ke dauke da su sun jikkata,” inji shaidan, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Shaidan ya ce an kai fasinjojin da suka samu rauni wani asibiti a yankin Okrika, bayan faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Mun tuntubi Baturen ’Yan Sandan Ruwa na yankin Bonny Island, SP Solomon Adeniyi, amma ya ce ba shi da hurumin yin magana a kan al’amarin.

A cewarsa, mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni, zai yi wa ’yan jarida bayani a kan abin da ya faru.

Mun yi kokarin samun SP Nnamdi Omoni, wanda muka yi ta kiran wayarsa amma bai dauka ba, bai kuma amsa rubutaccen sakon da muka aika masa ta waya ba game da al’amarin.

Amma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa da ke Bonny, Kwamanda Rafiu Oladejo, ya shaida mana cewa ya samu labarin abin, amma ba ya Bonny Island ba ne.

Duk da haka mun nemi jin ta bakin masu magana da yawun Babban Rundunar Sojin Kasa ta 6, da takwaransa da Runduna ta Musamman ta 115 ta Sojin Sama, duk a Fatakwal din, amma mun kasa samun magana da su.