✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin yaki ya yi wa fararen hula aman wuta a Yobe

Mutane da dama sun kwanta dama sakamakon lamarin a Jihar Yobe.

Fararen hula da dama sun rasu bayan wani jirgin yaki ya fado a garinsu ya yi ta feshin wuta a Karamar Hukumar Yunusari ta Jihar Yobe.

Safiyar Laraba ce mazauna kauyen Buhari da ke yankin suka wayi gari da ganin wasu jiragen yaki uku suna musu shawagi, daga baya daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta a kan wasu gidaje a garin.

Aminiya ta gano cewa yankin da lamarin ya faru na makwabtaka ne da Jamhuriyar Nijar kuma babu layin sadarwa.

An garzaya da mutane da dama ta lamairn ya ritsa da su zuwa babban asibitin da ke garin Geidam, inda ake ba su kulawa.

Ba a dai tatance asalin jirgin ba, amma Sashen Hausa na BBC ya ruwaito wani mazaunin yankin na cewa, “Ko a cikin gidanmu ma mun rasa mutum biyu”.

Mutumin ya ce, “Jirgin babba ne sosai irin na sojoji, amma ba mu san na ina ne ba”, ya kara da cewa, “Amma ni ba na gida lokacin, muna gefen gari, a kan idonmu komai ya faru.”

Mutumin, wanda ya ce a mamatan gidansu har da matar babansa da ’yar yayarsa ya bayyana cewa, “Da safe kamar karfe 8.30 ne abin ya faru, har zuwa lokacin da daya daga cikin jiragen ya fado wani bangaren na garin yana ta zubar da wuta, duk gidajen da ke wannan bangaren sai da suka lalace.”

A cewarsa, babu jami’in tsaron da ya je wajen, “don da akwai yaran Boko Haram da ke shawagi sosai a yankin”.