✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin yakin Birtaniya ya yi hatsari

An garzaya da matukan jirgin yakin zuwa asibiti, bayan hatsarin na safiyar Alhamis

Wani jirgin yaki, samfurin Hawk T1 mallakin Rundunar Sojin Ruwa ta kasar Birtaniya ya yi hatsari a safiyar Alhamsi a yankin Cornwall.

Ma’aikatar Tsaron Birtaniya ta tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin yakin na rundajar ta 736 daga RNAS Culdrose a lardin Lizard peninsula, sai dai babu wanda ya mutu.

“Matukan jirgin su biyu na samun kulawa daga jami’an lafiyar bayan sun yi saukar lema daga jirgin yakin. A halin yanzu ba za mu bayar da karin bayani ba,” inji Ma’aikatar tsaron.

Asibitin Cornwall ya wallafa a shafinsa cewa, “An dauki mutanen su biyu a wani jirgi zuwa Asibitin Derriford inda za a yi jinyar raunukan da suka samu… Har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da aiki a wurin da abin ya faru.”

Kamfanin mai jiragen daukar marasa lafiya ya ce, ya kai dauki ne bayan samu rahoton lalacewar “injin jirgin saman” a yankin Helston, kuma mutane biyu da ke ciki sun samu raununa.