Jonathan a Jam’iyyar APC (3) | Aminiya

Jonathan a Jam’iyyar APC (3)

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
    Ibrahim Malumfashi mfashi@yahoo.com

Wani abu da na tabbata jama’ar Najeriya ke bukata a halin da ake ciki yanzu shi ne canji, sai dai ga alama shugabannin da ke dauke da tarin tsintsiya a yanzu, canjin da kila suke neman su kawo wa kasar shi ne na ajiye Lema a dauki Tsintsiya a makwafinta. A lura duk irin shan rana da dukan ruwan sama da ’yan Najeriya suka yi ta fama da shi tun daga 1999 zuwa yau, ba shi ne abin damuwa ba. Idan shugabannin Lema za su sake sheka, su kasance kansiloli da ciyamomi da gwamnoni da ’yan majalisa da sanatoci da Shugaban Kasa da sauran mukarraban gwamnati dauke da tulin Tsintsiya a hannunsu, su a ganinsu, wannan shi ne canji. Idan kuma an natsu an yi nazarin abin da ke faruwa a halin yanzu za a ga alamun haka. Mece ce hujja?

Bari mu soma da wasu misalai na fili kafin mu leka na boye. A Jihar Kaduna, wadansu daga cikin tsofaffin shugabannin Lema da suka sake sheka zuwa Tsintsiya, an yi taron karbarsu, wadansu kuma daga cikin tsofaffin shugabannin har bude baki suka yi suna fada wa ’yan Tsintsiyar da suka tarbe su da su yafe musu laifin da suka yi musu a can baya. Wani da ya mike cewa ya yi, lallai mun san cewa a zaben da ya wuce mun cuce ku, mun hana ku ci zabe, mun sace akwatunan zabe, mun yi zurmuken kuri’u, domin mu tabbata Lema ta ci zabe, a yafe mana wannan laifi. Har nuna wani ya yi a cikin masu canja shekar da cewa shi ne dakaren sace akwatuna. Ya nuna wani ya ce shi ne gwanin canja alkalumma a cikin kwamfuta domin a yi zurmuken kuri’u. Duk wannan an yi haka ne domin a fahimci juna, a kuma yafe musu kafin su shiga cikin sabuwar Tsintsiyar da ke tashe yanzu.

A lura, irin wadannan gungun shugabannin su ne ke watayawa da neman matsayi a cikin Tsintsiya. Su ne za su kasance masu fada-a-ji nan gaba cikin jam’iyyar Tsintsiya. Su ne za su jagoranci al’ummar Tsintsiya a wasu sassa na Najeriya. Su ne za su zabi wadanda za su tsaya takara, su ci zabe, su kuma mulki al’umma. Su ne za su kasance canjin da ake nema. Ina canji a nan, in dai muna aiki da kwakwalwa? Shin canji me yake nufi? Malam Aminu Kano ya fasalta mana shi ba tun yau ba. Canjin da ke da muhimmanci ko yake tabbata a cikin al’umma, shi ne wanda aka yi watsi da tsofaffin hanyoyin da ke yin tarnaki ga ci gaban rayuwar al’umma, a kama sababbin matakan da za su kawo sabuwar rayuwa da ci gaba. Amma idan an lura da kyau sai a ga cewa kamar a yanzu, shara ce ake yi cikin duhu, ba a san mai rike da Tsintsiyar ba, balle kuma abin da ake sharewa ko sharowa ko inda za a kai sharar. A cikin tsari irin wannan, tamkar wankin fararen tufa ne da ruwan tabo!

Idan kuma wannan bai sa mu yin tunanin ta-natsu game da irin hargidiballen da ke faruwa ba, to me za mu ce game da yadda a wasu jihohin ake ta faman sa-in-sa tsakanin wasu gwamnonin da suka ajiye Lema suka dauki Tsintsiya da sauran al’ummar da suka tarar a cikin jihar? Me ya faru a jihohin Kano da Sakkwato da Adamawa bayan gama zabe? Ko kafin wadannan gwamnoni su canja sheka, akwai wadansu zaune daram a cikin sabuwar shekar da suka matsa sai sun samu wurin zama a ciki, yanzu takaddama ce ta yi yawa, su wane ne ya dace su ja ragamar Tsintsiyar, ’yan gida na asali ko kuwa sababbin zuwa? Su wa za su zabi wadanda za su yi takara, ’yan Mowa ko ’yan Bora? Su wa za su yi takarar, ’yan asalin cikin gida ko kuwa agololi? Duk wadannan abubuwa ya dace mai bin al’amurran siyasa da kasa ya lura da su, ya kuma yi wa kan sa kiyamullaili tun kafin a yi masa sakiyar da ba ruwa.

A cikin irin wannan kwamacala, ba ma ganin cewa za a yi abin nan ne da Hausawa ke cewa ba cinya ba, kafar baya? Ba ma jin cewa idan Lema ta saje da Tsintsiya muna nan dai yadda muke, jiya kamar yau? Ba ma jin cewa idan har tuta da alamun jam’iyya ne suka canja, to ba canji ba ne aka samu, kila sai dai caji da cuta da cutarwa?

Wani abin kara la’akari shi ne, irin yadda masu sukuwa a kan dokin da Tsintsiya ta samar suka kasance bara-gurbi a tsawon lokaci. Akwai wadanda tun asalinsu ’yan Lema ne, suka gudu zuwa wasu gidajen na tsawon shekaru, daga baya suka sake tarewa a jikin Lema, yanzu kuma suna ta daga Tsintsiya. Haka kuma ko a yanzu abin da ke faruwa ke nan; ba mutane ake nema su shigo cikin Tsintsiya ba; ba tallata kyawawan manufofin Tsintsiya ake yi ba; ba ana yawo da fuskokin da za su sa talaka ya dara ba ne in ya gan su, domin yana tsammanin wadannan fuskoki su ne masu agaza masa, ba masu danne shi ba. A tsarin da duk lokacin da talaka ya daga ido ya ga masu neman kawo canjin tinjim a cikin Tsintsiya, sa’annan sun kasance daga Lemar da ta kasa kare su daga dukan ruwan sama ko kuma bugun rana a tsawon shekaru da wuya ya aminta da duk wani holokon alkawari ko kuma canjin da kila ba zai gani a kasa ba!

Tambayar da wadansu ka iya ita ce to ina mafita daga wannan gamaden siyasa? Me talaka zai tsinkaya daga hadarin da ya hadu a yanzu a cikin sararin samaniyar siyasar kasar nan, daga yanzu zuwa nan gaba? Me talakan Najeriya ya kamata ya yi ko ya sani dangane da irin wannan harbar-ta-Mati da ake yi ko ake neman a yi masa dangane da shugabancin kasar nan? Sa’annan uwa-uba wace rawa ce zai iya takawa wajen kawo wa kansa da kasa canjin da ya dace da ita, idan al’amurra sun ki ci, sun ki cinyewa?

Za mu ci gaba