Jonathan a Jam’iyyar APC (4) | Aminiya

Jonathan a Jam’iyyar APC (4)

    Ibrahim Malumfashi

Kila amsa irin wadannan tambayoyi ba daga gare ni ya kamata su fito ba, amma kuma muna iya hada karfi da karfe waje daya mu ga ko za mu iya samar da mafita daga wannan hargidiballe. Sai dai kafin mu yi nisa mu fahimci wani abu guda da ke muhimmanci. Najeriya a matsayin kasarmu, ta kowa da kowa ce, daga shugabannin har zuwa wadanda ake shugabanta, ke nan ba wani da zai ce shi ne ya mallake ta, saboda haka shi ne zai yi mata alkiblar da yake ganin ita ta dace da ita. Shugabannin siyasa suna bisa matsayi ko mukaman da suke kai ne a matsayin wakilai na sauran al’umma, saboda haka don mun zabe su ko sun samu kansu a bisa irin wannan matsayi ba yana nufin an ba su lasisin da za su yi yadda suka ga dama ba ne, dole ne su yi aiki domin al’umma ba domin kyautata wa kansu ko wadansu ’yan tsiraru ba. Idan haka ne tsarin ya tanada, wanda kuma hakan ne, ke nan mulki a hannun al’umma yake ba wadanda aka zaba ko suka samu kansu bisa kowane irin matsayi ba.

A bisa irin wannan tunani, abubuwan da ya dace mu mayar da hankali a kai a cikin irin wannan tarmahaha ta Lema da Tsintsiya da kuma tafarkin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma aiki da kuma ingantaccen tsarin siyasa shi ne mu koma bisa turbar aiki domin al’umma daga mutanen da al’umma suka amince da su a matsayin natsattsu, kamilai, yardaddu, masu hangen nesa da neman mafita ga al’umma. Kada inji wani ya ce ai ba mu da su, domin kuwa suna nan jibge a cikin tsibin mutanen da ke cikin kasar nan, sai dai ba mu damu ko ba mu kula da nema da hulda da su ba ne, ganin cewa sankara ta kame kowane bangare na rayuwar yau da kullum ta ’yan Najeriya. Me nake so mu yi ke nan? Mu yi watsi da jam’iyya mu kama gaskiya! Wacce ce gaskiyar? Gaskiya irin ta marigayi Aminu Kano, irin ta marigayi Obafemi Awolowo, irin ta tsohon Gwamnan Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa, gaskiya irin ta Janar Muhammadu Buhari da irinsu da dama a cikin kasar nan. Duk da cewa ire-iren wadannan mutane da na lissafo suna da jam’iyyun siyasa da suke tokabo da su, za a samu cewa su din ne jam’iyyun siyasar, ba siyasar ce su ba! Manufofi da tadoji da kimar siyasar na tattare da su da mabiya bayansu a koyaushe. A duk lokacin da suka fadi zance ko suka yi alkawari al’umma na amincewa da su domin sun sansu da gaskiya da rikon amana. Shi ya sa a siyasar irin wadannan mutane ake ganin karancin jam’iyya tattare da su, amma kuma suna samar da yawaitar mutane na kwarai daga jikinsu. A zamanin su Aminu Kano da jam’iyyun Makulli/Mabudi da Gida da Masara, kowa ya san matsayin kowacce, musamman a nan Arewacin Najeriya. Haka abin ya kasance a zamanin NEPU da NPC a zamanin su Sardauna. Mutane su ne jam’iyya, su ne gwamnati, su ne kuma masu fada-a-ji, saboda kowace jam’iyya da manufofin da suke jan ra’ayin al’umma zuwa gare ta, su kasance tare da ita komai rintsi, ba haka nan suke kara-zube ba.

Irin wannan ne ya gina so da kaunar Awolowo ga mutanensa, haka kuma irin su Balarabe Musa da kuma yanzu Shugaba Muhammadu Buhari. Har yau din nan, abin da Balarabe Musa ke kira ga al’umma shi ne, kowa ya bar batun Tsintsiya da Lema ya koma ga Mabudi/Makulli a matsayin mai ceto da cetarwa.  Ba wani abu ya sa yake furta haka ba, domin ya san cewa manufofin PRP da ya dage a kai su ne za su iya fitar da kasar daga cikin halin  kaka-ni-ka-yi, sa’annan uwa-uba ba kowa ba ne zai iya aiwatar da manufofin, sai mai gaskiya.

Wannan shi ne gaskiyar zance, kuma shi ne muke gani a tsarin siyasa irin ta Buhari, wadda kuma jama’a da kansu ke fada tun daga 2003 zuwa yau game da shi da wadansu.

Shin jam’iyya ce ta sa ake son shugabancin Buhari a wasu sassan kasar nan? Shin jam’iyya ce ta sa ake kewar Bola Tinubu a inda yake a Najeriya? Shin jam’iyya ce ta sa ake yabawa da ayyukan Rabi’u Musa Kwankwaso, a lokacin yana Gwamnan Kano ko Fashola a lokacin yana Gwamnan Legas? Ko alama! Ba ruwan jam’iyya, in ma akwai ruwan jam’iyyar a wasu wurare to Shugaba shi ya fi damawa domin ya yarda da abin da yake yi, jama’a kuma sun aminta da shi; kuma zai gabatar da aiki ko da jam’iyya ko ba jam’iyya, domin aikin ya zo yi ba sharholiya ba. Wanda shi ke da muhimmanci.

Wannan ne ya sa tunda ake ta fafutikar kawo sauyi a kasar nan, amon da ya fi tashi, musamman a nan Arewa shi ne, ba a son kowa ‘Sai mai gaskiya!’ Ba wanda ke cewa sai ‘Jam’iyya mai gaskiya,’ in ma an ji wadansu sun fadi haka, to saboda mai gaskiyar ne, ba don komai ba, domin a yawancin tunanin mutane ba ruwansu da wannan jam’iyya, sai mai gaskiya. Idan da muna da gaskiya ko aiki da ita da ba mu ga tambelen da wadansu ’yan siyasa ke faman yi daga wannan jam’iyya zuwa waccan ba, ba matsaya guda, sa’annan a ce kuma ana neman canji. Idan ba a yi hankali ba duk sai an koma cikin Tsintsiya cikin wayo ko kuma dabara, a yi ta shara, mai tada kura, sa’annan a ce canji ake nema!

Gaskiyar batu shi ne, ba mu da jam’iyyu sai masu murkushe al’umma da sunan jam’iyyun, suna kuma yin haka ne ganin cewa sai da jam’iyyun ne kurum za a iya takarar zabe, a ci zaben ko kuma a ce an ci zabe. Ba su damu da zabar wadanda za su bauta wa al’umma ba, in har sun zabo wadanda ke da kishin kasa da son al’umma su yi shugabanci to kila cikin rashin sani ne ko mantuwa, kuma an rika samun takun-saka a tsakanin Shugaban da wadanda suka dora shi ko ita.

A irin wannan tsari ba abin da ya rage sai a koma ga tsarin da hankali zai iya karba, kuma zuciya na so. Wanne ne wannan tsarin?

Za mu ci gaba