Jonathan a Jam’iyyar APC (5) | Aminiya

Jonathan a Jam’iyyar APC (5)

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
    Ibrahim Malumfashi

Kamar yadda muka fara bayanin a baya, gaskiyar batu shi ne, ba mu da jam’iyyu sai dai kila masu murkushe al’umma da sunan jam’iyyun, suna kuma yin haka ne ganin cewa sai da jam’iyyun ne kurum za a iya takarar zabe, a ci zaben ko kuma a ce an ci zabe. Ba su damu da zabar wadanda za su bauta wa al’umma ba, in har sun zabo wadanda ke da kishin kasa da son al’umma su yi shugabanci, to kila cikin rashin sani ne ko mantuwa, kuma an rika samun takun-saka tsakanin shugaban da wadanda suka dora shi ko ita.

A irin wannan tsari ba abin da ya rage sai a koma ga tsarin da hankali zai iya karba, kuma zuciya na so. Wanne ne wannan tsari?

Tsarin nan shi ne tsarin da talakawa ne ke jan ragamar siyasa da ’yan siyasar. Tsari ne da mutanen kasa su ne jam’iyya ba wadansu ’yan tsiraru da ke hayewa kan akawal ko dandan mulki su ce su ne masu fada-a-ji ba. Tsari ne da al’umma za su ce ga yadda suke so a yi, a kuma tabbata an yi, ana so ko ba a so! Tsari ne da ke nuni zuwa ga tafarkin ci gaba, ba tafarkin cika aljihu da zama ’yan ma’abba ba.

Wannan tsari ba wani tsari ba ne da ya wuce al’umma ta yi wa kanta kiyamullaili, su zabi mutane nagari domin su jagorance su, ko da kuwa daga jam’iyyar Shaidan suka fito, in dai sun tabbata su ne mafita ga al’ummar. Sai dai a lura, in an zabi irin wadannan mutane, to, ya dace kuma a tabbata ana bin su da hajar mujiya a koyaushe, domin a tabbatar ba su kauce hanya ba a kowane mataki na mulki da jagorancin al’umma.

Ta yaya hakan zai iya kasancewa? Mu sani a yau ba mu da zabi a tsakanin Tsintsiya ko Lema ko wani abu makamancin haka, domin kuwa duk kanwar ja ce. Wanda yau ya kasance dauke da Tsintsiya gobe kana iya ganinsa a cikin Lema, kuma ya yi maka kiri-da-muzun cewa nan ne matattarar alheri. Haka wani na iya gajiya da zama cikin inuwar Lemar, ya fito cikin rana gatsar ya fara shara da Tsintsiya ya ce maka ai ba komai cikin Lemar sai kyankyasai da bara-gurbi, alhali kuwa nan inda yake zaune da Tsintsiyar bara-gurbin sun fi yawa, kyankyasai kuwa tuni suka yi gida suka zaune!

Dangane da haka ni a tawa tsinkayar akwai abubuwa kamar guda hudu da za mu iya yi ko matakan da za mu iya bi domin kaiwa ga tudun-mun-tsira.

Abu na farko shi ne mu tabbata in lokacin zabe ya yi mun zabi wadanda suka dace da zamanin da muke ciki, ma’ana, wadanda mun tabbatar za su agaza wajen raya al’umma, ba wadanda za su kashe ta ba. Su wane ne wadannan mutane? Har yanzu akwai na kwarai a cikin al’ummarmu, har yanzu akwai masu kishin ci gaban al’umma ta kowace irin fuska, suna nan jingim, su ya dace mu fita nema ko da ba sa siyasar domin jawo su, su maye gurbin wadanda muke ta faman shan wahalarsu a halin yanzu.

Ba jam’iyyar siyasa ya kamata mu damu da ita ba, a’a, rukunin mutanen da za su fitar da A’i daga sana’ar rogon da take ta fama ita, kuma na tabbata akwai su.

Idan kuma mun zabe su, mu tabbata mun bar su domin su yi mana aikin raya kasa ba aikin raya mana aljihunanmu ba. Ma’ana, yadda talakawa ke biye wa son rai, suna biye da wadanda suka zaba domin su ba su taro ko sisi ko kuma su biya musu bukatansu, in ya so aikin raya kasa ko oho yana da cikin matsalolin da ke sa ’yan siyasa ke yi mana wa-ka-ci-ka-tashi. Mu barsu da dukiyar kasa da dukiyarmu, su yi aikin da aka tanada, wannan shi ne zai taimaka wajen kawo abinci ga wanda ke bukata, aikin yi ga wadanda suke bukata ko kuma zaman lafiya a cikin kasa.

Idan mun daure mun hadiye kwadayi, to, za mu iya matsa wa wadanda muka zaba su yi wa al’umma aiki ba wandaka ba!

Haka kuma ya dace mu kasance masu sa ido ba wai sa’idawa ba game da yadda ake mulkarmu ko ake gudanar da lamuran dukiyarmu a kowane mataki na rayuwa. Wannan aikinmu ne domin mu ne masu zabe da kuma kulawa. Wanda aka zaba ba gunki ba ne ko wani dodo, idan mun dage wajen ganin an yi yadda ya dace, to dole za a yi, idan kuma mun mika ragamar mulkin ga wadansu, muka sa kwadayi da rashin kishin kasa a rayuwarmu, to duk bala’in da ya auka mana, mu muka ja wa kanmu. Hausawa na cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga,

Daga karshe kuma, Hausawa na cewa ba a fafe gora ranar tafiya. Shekarar zabe ba ta riga ta karaso ba, nan da shekarar 2023 muna da akalla shekara 3, ina wadanda muka zaba a halin yanzu, ai suna nan ba su sauka ba, me zai hana mu fara sa ido tun yanzu. Mu bi duk wani Kansila ko Ciyaman ko Kantoma ko dan Majalisar Jiha ko Gwamna ko dan Majalisar Tarayya ko Sanata ko Shugaban Kasa mu ce ina awalajar dimokuradiyyar da aka yi mana alkawari? Wane aiki kuka yi da za mu dora ku bisa wannan mukami ko mu sake ba ku wani sabo don ku ci gaba da mulki? Mu tambaye su wane aiki suka yi da dukiyar da muka damka musu amana a cikin tsawon shekaru? Wadanne dokoki suka yi domin ciyar da kasa gaba? Ina biliyoyin nairorin da ake dauna wa gwamnonin jihohinmu suke shiga, wajen raya kasa ko aljifan wadansu kalilan daga cikin al’umma? Me sanatocinmu ke yi a Abuja da tarin dukiyar da aka tanadar musu a matsayin albashi? Me ’yan siyasa suka yi mana na a-zo-a-gani? Me jam’iyyun siyasar suka yi mana da za mu sake dora su bisa karagar mulki?

Wannan shi ne abin da ya dace da mu a halin yanzu, domin kuwa ba mai fitar da talaka daga cikin kangin da yake ciki face shi talakan da kansa, ba kuma wata hanya da ta dace mu bi domin kawo sauki, face mu rika yin tambayoyi, domin ta haka ne za mu samu amsar badakalar rayuwar da muke ciki. Allah Ya taimaka!

Mun kammala