✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jordan ta la’anci wulakancin Isra’ilawa a Masallacin Kudus

Lamarin ba wani abu ba na face ketare duk wata iyaka ta doka a duniya a masallacin mai dadadden tarihi.

Gwamnatin Jordan ta yi Allah-wadai kan abin da ta ce Isra’ilawa na wakulankanta Masallaci mai alfarma da ke birnin Kudus, wato masjid al-Aqsa.

A ranar Talata ne dai Kasar Jordan ta yi Allah-wadai da yadda wasu ’yan Isra’ila masu tsattsauran ra’ayi ke ci gaba da keta alfarma da kuma kutsa kai cikin harabar masallacin da ke karkashin kariyar ’yan sandan Isra’ila.

Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan, Sinan Majali, ya bayyana cewa, wannan lamari ne da ya wuce gona da iri.

Ya ce lamarin keta alfarmar masallacin na kara ta’azzara a yayin da Isra’ila ke ci gaba da sauran ayyukan ta’addanci a harabarsa ta kuma sanya wa masu ibada takunkumi.

Majali ya ce wannan lamari abin Allah-wadai ne da ba shi wata kamanceceniya face ta cin zarafi da ketare duk wata iyaka ta doka a duniya a masallacin mai dadadden tarihi.

Majali ya yi nuni da cewa, ba za a taba samun zaman lafiya ba muddin aka ci gaba da keta alfarmar wurare masu tsarki da kuma hare-haren da Isra’ilawa ke kai wa yankunan Faladinawa.

Ya kara jaddada cewa, harabar masallacin da kewayenta duk wuri ne na ibada da ya kebanta domin musulmai zalla, saboda haka alhakin kula da masallacin ya rataya ne kadai a wuyan Sashen Kula da Harkokin Masallacin Kudus.

Ya yi kira ga Gwamnatin Isra’ila wacce ta mamaye masallacin, da ta gaggauta dakatar da duk wasu ayyuka da take aiwatarwa da nufin sauya tsari na dokokin alfarma da suka kebanta da masallacin.