✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juliet Ibrahim: Nan gaba Kannywood za ta hada kafada da Hollywood

Juliet Ibrahim ’yar fim ce a kasar Ghana, ta lashe kambun Mace Mafi Kyau a Yammacin Afirka na Mujallar A-Listers ta 2013. A kwanakin baya…

Juliet Ibrahim ’yar fim ce a kasar Ghana, ta lashe kambun Mace Mafi Kyau a Yammacin Afirka na Mujallar A-Listers ta 2013. A kwanakin baya ta fara fitowa a fim din Hausa mai suna ‘Ladan Noma.’ Aminiya ta tattauana da ita game da yadda ta ga masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood) da kuma yanayin da ta samu kanta a lokacin da take aikin fitowa a fim din. Ga yadda hirar ta kasance:

n ‘Yar wasa Juliet IbrahimZa mu fara da tarihin rayuwarki?
An haife ni a Ghana, mahaifina din kasar Lebanon ne, mahaifiyata kuma ’yar kasar Ghana. Ni ce ta farko a wurin mahaifana, amma ina da kanne uku, mata biyu da kuma namiji. Na yi makarantar firamare a Lebanon, na kuma yi makarantar sakandare a Kwaddibuwa, sannan na yi makarantar gaba da sakandare a Ghana, inda na karanta yarukan Ingilishi da Faransanci da kuma Safaniyanci.
Wacce shekara kika fara fitowa a fim, sannan me ya ja hankalinki kika shigar harkar fim?
Na fara fitowa fim ne a shekarar 2005 a wani fim mai suna ‘Crime to Christ’ na wani jarumi dan kasar Ghana mai suna Majid Michel. Amma fim dina na farko a masana’antar fina-finai ta Najeriya (Nollywood) shi ne ‘Yankee Boys.’ Dangane da abin da ya ja hankalina har na shiga harkar fim kuwa shi ne, tun ina karama nake da sha’awar yin fim, domin ina ganin masana’antar a matsayin fagen da za ta ba ni damar isar da sakon da nake son isarwa cikin sauki. Kuma cikin ikon Allah ban sha wahala wajen samu damar shiga harkar fim ba.
Yaya kika ji a lokacin da aka ce za ki fara fitowa a fim din Hausa?
A lokacin da muka je kauye na kasance cikin dari-dari, musamman bayan na karanta labarin fim din, inda na ga za a dauki wani bangare na fim din a kauye. Ina kaffa-kaffa ne saboda na karanta a labarai dangane da hare-haren da mayakan Boko Haram suke kai wa kauyuka, sai ga shi kuma za a dauki wani bangare na fim din a kauyen da ke Arewacin Najeriya ne.
Ta yaya aka shawo kanki har kika je kauyen don daukar fim din?
Na fara samun natsuwa bayan Uzee Concpet ya tabbatar mini da babu abin da zai faru da ni. A karshe na samu kwanciyar hankali bayan na ga yadda abubuwa suka gudana a kauyen, musamman ma yanayin yadda ’yan kauyen suka rika farin ciki da ganinmu. Sannan na duba yanayin kauyen sai na ga babu wata fargaba ko razana a tattare da su, hakan ya tabbatar mini suna cikin kwanciyar hankali, sannan ba sa fuskantar wata barazana.
Yaya za ki bayyana wa masu karatu gamsuwar da kika samu dangane da rawar da kika taka a fim din?
Na samu gamsuwa dangane da rawar da na taka a fim din, saboda ina son sabon abu, kuma rol din da na hau a fim din sabo ne, hakan ya gamsar da ni sosai, domin ya nuna mini na cika jaruma tun da zan iya hawa rol din sabon abu da ban taba saninsa ba.
Wane kalubale kika fuskanta yayin daukar fim din?
kalubalen da na fuskanta shi ne lokacin da nake magana da Hausa a cikin fim din, duk da kasancewar haruffan Hausa ba su da tsauri, amma da yake ban taba magana da Hausa ba sai abin ya ba ni wahala kadan, amma kasancewar ina da basira wajen kwaikwayo, sai basirar ta taimaka mini wajen cin ma burina a fim din. Sannan kada ka manta a makaranta na karanta yarukan Ingilishi da Faransanci da kuma Safaniyanci sai hakan ya ba ni damar iya magana da Hausa cikin sauki.
Yaya kike ganin Kannywood a nan gaba?
A gaskiya na samu gamsuwa dangane da yadda suke gudanar da ayyukansu, suna da kayan aiki, sannan suna da tsari, babu wanda yake shiga aikin wani. Kyamarar da suke amfani da ita, ita ce ake amfani da ita a Hollywood. Idan har suka ci gaba a yadda suke gudanar da ayyukansu, sannan suka samu wadanda suka zuba jari a harkar, nan gaba Kannywood za ta hada kafada da Hollywood.
A shekarun baya kin lashe kambun Mace Mafi Kyau a Yammacin Afirka ta Mujallar A-Listers ta shekarar 2013, yaya kaka ji da wannan nasara?
A gaskiya na samu kaina cikin farin ciki, wannan ya nuna mini ina kan turba mai kyau, duk da cewa mahaifana ’yan kasashe mabambanta ne.
A kwanakin baya an rika yamididi da batun aurenki har aka ce ke ce kika kashe auren saboda ba ki samun kulawa daga tsohon mijinki, an ce kin ma aure shi ne saboda kin samu ciki da shi, me za ki ce a kan hakan?
Na samu kaina cikin tsomomuwa a wannan auren, mahaifansa ba su sona, ba su ma halarci bikin aurenmu ba, don haka na fuskanci matsaloli daban-daban; a karshe dai na tabbatar da kwalliya ba za ta biya kudin sabulu game da auren ba, shi ne aka raba shi.
Ga shi kina da da kuma yawancin lokacin jarumai ya fi tafiya a wurin daukar fim, ko yaya kike kula da dan naki?
dana yanzu ya shekara 4, yana zuwa makaranta a lokacin da nake wurin daukar fim ko wani aiki nawa, ya san cewa mahaifiyarsa tana fita aiki ne don ta dauki dawainiyarsa, ba kowane lokaci nake wurin daukar fim ba, na san yadda nake kula da iyalina da kuma aikina.
Kin fito a fina-finai tare da jaruman fina-finan Najeriya da kuma na Ghana, a zuwa yanzu wane jarumi kika fi jin dadin aiki da shi?
Wannan tambayar taka tana da matukar daure kai, babu jarumin da ba shi da hazaka wajen fitowa a fim, kowa ya san aikinsa, sannan dukkansu suna daraja ni hade da ba ni muhimmanci. Ni ma ina ba su dukkan kulawa.
Kun fito tare da jarumi Rabi’u Ibrahim (Daushe), ko yaya za ki bayyana yadda kika ji aiki da shi?
A gaskiya yana da hazaka da kuma jajircewa wajen ganin ya yi abin da darakta ya fada masa ya yi, bai ba ni wahala ba, amma yana da surutu, sai dai hakan ya taimaka masa wajen bayar da abin da ake so a fim din.
Daga karshe ko kina da wani kira da kike so ki yi?
Kirana bai wuce ga iyayen da suke tsangwamar matar dansu ba, su fahimci hakan ba komai zai kawo ba face farraka zaman aure, a karshe a rika da-na-sani. Ina so iyaye su rika jan surukansu a jiki, ta haka ne dansu zai samu salama, sannan aure ya yi karko.