✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juventus na shirin gwanjon Pjanic, Costa da Higuain

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus tana shirin yin gwanjon ‘yan wasanta guda hudu da nufin rage tasirin da coronavirus ta yi a kan lalitarta. ‘Yan…

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus tana shirin yin gwanjon ‘yan wasanta guda hudu da nufin rage tasirin da coronavirus ta yi a kan lalitarta.

‘Yan wasan da take shirin sayarwa a karshen kakar wasannin dai sun hada da dan wasan tsakiya Miralem Pjanic, da Douglas Costa, da Gonzalo Higuain da Sami Khedira.

Shugaban Sashen Wasanni na kungiyar Fabio Paratici ne ya gabatar da wasu sabbin tsare-tsare a kungiyar da za su rage kashe kudi wurin biyan ‘yan wasa.

Yunkurin nashi dai zai tabbatar cewa babu dan wasan da za a biya sama da fam miliyan shida a shekara.

A halin da ake ciki dai kungiyar tana da manya-manyan ‘yan wasa da albashinsu ya haura hakan.

Yunkurin sayar da ‘yan wasan dai wani mataki ne da jaridar Daily Mail ta bayyana a matsayin mai wahalar gaske bisa la’akari da ‘yan wasan da abin zai shafa, amma hakan ya zama dole saboda kungiyar ta samu damar tsayawa da kafafunta a halin da ake ciki.

Ko Barcelona za ta dauki Pjanic?
Tuni dai jaridar Daily Mail ta rawaito cewa kungiyar Barcelona ta baza taru saboda daukar Pjanic idan har kungiyar Juventus ta sa shi a kasuwa.

Bayan kungiyar ta Barcelona, kungiyoyin Chelsea da PSG ma sun nuna aniyarsu ta dauko dan wasan, dan asalin kasar Bosnia.

Dan wasan, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 60 a kasuwar ‘yan wasa, yana son ci gaba da zama a kungiyar ta Juventus.

Barcelona na zawarcin Lautaro Martinez
Jaridar Mundo Deportivo da ke kasar Spaniya ta rawaito cewa kungiyar Barcelona ta sake kulla aniyar dauko dan wasan gaba na kungiyar Inter Milan Lautaro Martinez.

Martinez, wanda dan asalin kasar Argentina ne, yana cikin ‘yan sahun gaba da kungiyar Barcelona take son sayowa kafin kakar  badi.

Jaridar ta Mundo Deportivo ta kuma rawaito cewa a makon nan ne hukumomi a Camp Nou za su yi kokarinsu wurin shawo kan kungiyar da ma dan wasan ya sauya sheka zuwa kungiyar ta Kataloniya.

Kungiyar Barcelona dai ta samu kwarin gwiwa ne saboda tuni dan wasan ya nuna sha’awarsa ta sauya sheka zuwa taka leda a Spaniya.

Manchester United za ta yi kokarin daukar Koulibaly

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyana shirinta na dauko mai tsaron baya na kungiyar Napoli, Kalidou Koulibaly.

Jaridar Daily Express ta bayyana cewa kungiyar ta Manchester United tana fatan gyara tsaron bayanta ne da dan wasan dan shekara 28 daga kasar Senegal.

Ko ina Karius zai koma?
Mai tsaron gida na kungiyar Liverpool Loris Karius wanda aka tura aro zuwa kungiyar kwallon kafa ta Besiktas ya shiga halin rashin tabbas tun bayan da kungiyar ta katse kwantiraginsa ana tsakiyar kakar wasanni.

Karius din, wanda shi ne Liverpool ta je wasan karshe na Gasar Zakarun Turai da ta sha kashi a hannun kungiyar Real Madrid, a wani abu da ake gani kamar sakaci, ya sa kungiyar ta gaza lashe gasar a shekarar 2018, lamarin da ya sa kungiyar ta tura shi aro ta maye gurbinsa da Alisson Becker dan kasar Brazil.

Jaridar Daily Star ta bayyana cewa Karius din ba zai dawo atisaye tare da kungiyar Liverpool ba duk da katse kwantigarinsa da kungiyar Besiktas din ta yi.

Man City na bukatar David Silva ya tsawaita kwantiraginsa

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City tana sa ran dan wasanta, David Silva, zai amince da bukatar da ta mika masa ta tsawaita kwantiraginsa ta yadda zai kammala kakar wasanni a kungiyar.

Silva dan shekara 34 yana cikin ‘yan wasan da suka fi dadewa suna taka wa kungiyar leda.

Jaridar ESPN ta rawaito cewa kwantiraginsa na yanzu zai kare ranar 30 ga watan Yuni.