✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juventus za ta maye gurbin Ronaldo da Hazard, Chelsea za ta dauki Jules Kounde

Atletico da Barcelona na takarar daukar Bernardo Silva.

Yayin da Cristiano Ronaldo ke ya koma Manchester United, rahotanni sun bayyana cewa Juventus ta tuntubi  Real Madrid don dauko Eden Hazard a matsayin aro. MARCA

Juventus na bukatar wanda zai maye gurbin Ronaldo kuma rahotanni sun tabbatar cewa ta nemi Eden Hazard a matsayin aro daga Real Madrid.

Akwai yiwuwar LiverpoolLeeds da Aston Villa su nemi daukar dan wasan Sampdoria Mikkel Damsgaard, sai dai Tottenham ta daina zawarcin dan wasan mai shekara 21, wanda ya murza wa kasarsa leda a gasar Euro 2020.(La Repubblica via Sport Witness)

Har yanzu Paris St-Germain ba ta bayar da amsa ga bukatar Real Madrid ta daukar dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22 ba, yayin da kungiyar ta La Liga ta kayyade ranar Litinin a matsayin wa’adi na karshe ga kungiyar da ke murza Ligue 1 kan ko ta amince ko kuma ta ki amincewa da tayinsu. (Marca)

Sevilla ba za ta amince da kasa da yuro miliyan 80 kan dan waan Faransa Jules Kounde ba.

Ana rade radin Chelsea za ta nemi daukar dan wasan mai shekara 22 bayan sayar da Kurt Zouma, mai shekara 26, ga West Ham. (Marca )

West Ham na dab da kammala biyan fam miliyan 25 domin daukar dan kasar Croatia Nikola Vlasic, mai shekara 23, daga CSKA Moscow(Guardian)

Aston Villa na shirin bayar da fam miliyan 15 domin daukar dan wasan Liverpool Curtis Jones, mai shekara 20, wanda har yanzu bai buga wa the Reds a kakar bana ba. (Sun)

EvertonBrightonLeeds da Crystal Palace suna fafatawa domin daukar dan wasan Manchester United da Wales Daniel James, mai shekara 23, wanda aka amince ya bar Old Trafford yayin da dan wasan Portugal mai shekara 36 Cristiano Ronaldo ya dawo United daga Juventus(Star)

Everton tana tattaunawa domin daukar dan wasan Venezuela Salomon Rondon daga kungiyar kasar China Dalian Professional. Kocin Everton Rafael Benitez ya taba jagorantar dan wasan mai shekara 31 a China da Newcastle. (Sky Sports)

Watford tana tattaunawa da Birmingham game da sayar da dan wasa mai shekara 33 wanda shi ne kyaftin na kungiyar Troy Deeney. (Athletic – subscription required)

Juventus za ta nemi daukar dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Belgium Axel Witsel, mai shekara 32, yayin da Massimiliano Allegri yake son inganta tsakiyarsa. (Sky Sport – in Italian)

Kungiyar Everton da ke neman dauke dan wasan baya na Rangers, Nathan Patterson ta hadu da fushin zakaran ta Sikotlan, kamar yadda kafar labarai ta the Liverpool Echo ta ruwaito.

Everton wadda ake yi wa lakabi da Toffees tana neman karfafa bayantsa ta gefen dama, wannan ya sa take zawarcin dan kwallon zuwa filin wasa na Goodison Park.

Sai dai duk da kyakkyawar alakar da take tsakanin manajojin kungiyoyin biyu Rafa Benitez da Steven Gerrard sun gaza taimaka wa Patterson ya koma Everton a wannan kaka.

Kungiyar Atletico Madrid ta cimma yarjejeniyar sanya hannu don daukar dan wasan gaba na Kungiyar Hertha Berlin, Matheus Cunha Goal.

Dan shekara 22 zai koma Wanda Metropolitano ne a kan Yuro miliyan 30, (Fam miliyan 26 ko Dala miliyan 35) bayan an gama cim-ma matsaya a kan kwantaragin nan da ’yan kwanaki.

Everton ma ta so sayen Cunha, amma sai ya nuna ya fi son zuwa gasar La Liga.

Kungiyoyin Atletico Madrid da Barcelona suna takara wajen sayen dan wasan tsakiya na Manchester City, Bernardo Silva – Sport Mole.

Pep Guardiola ya tabbatar da cewa dan shekara 27 din yana kokarin barin filin wasa na Etihad a kakar bana.

Atletico da Barca duka suna duba yiwuwar sayen ko daukar aron Bernardo, wanda yake da sauran shekara hudu a kwantaraginsa.

Dan wasan tsakiya na West Ham, Declan Rice yana ci gaba da zama wanda Manchester United take ‘fatar dauka’ kamar yadda kafar labarai ta Manchester Evening News ta bayyana.

Ta ce, Ole Gunnar Solskjaer zai so ya kara samun zabi a kungiyarsa kafin karewar wa’adin kasuwar ’yan kwallo.

Real Madrid tana kai bara ga Laporte dan wasan baya na Kungiyar Manchester City, Aymeric Laporte yana cikin ’yan wasan da Kungiyar Real Madrid take kai wa bara, a cewar rahoton jaridar Mundo Deportivo.

Dan kwallon dan kasar Spain, ba ya jin dadin gasar Firimiyar Ingila kuma akwai yiwuwar a ba shi dama a filin wasa na Santiago Bernabeu.