✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin mulki: Sojojin Sudan sun hallaka masu zanga-zanga 2, sun raunata 80

Mutanen dai na zanga-zanga ne don nun kin jinin juyin mulki.

Babban Kwamitin Likitotcin Sudan ya tabbatar da kisan mutum biyu sakamakon harbin bindigar da sojoji suka yi musu, wasu 80 kuma suka jikkata yayin zanga-zanga a birnin Khartoum.

Mutanen dai na zanga-zangar ne don nuna kin jinin juyin mulkin da sojojin suka yi a kasar ranar Litinin.

Dubban mutane ne suka fantsama titunan biranen Khartoum da Omburman bayan kama Fira Ministan kasar, Abdallah Hamdok da sauran kusoshin gwamnatin kasar da sojojin kasar suka yi.

Har zuwa yanzu dai babu wanda ya san hakikanin wajen da aka kai Fira Ministan bayan ya ki fitar da sanarwar nuna goyon bayan juyin mulkin, kamar yadda Ma’aikatar Yada Labaran kasar ta sanar.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar, Janar Abdel Fattah Al-Burhan daga bisani dai ya fitar da sanarwar rushe gwamnatin kasar sannan ya sanar da kafa dokar ta-baci.

Kasar Sudan dai ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan da ya wuce wanda ya kara tsamin dangantaka tsakanin sojoji da fararen hular da ya kamata su rika raba madafun iko a tsakaninsu.

Hakan dai ya biyo bayan kafa gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa tun bayan hambarar da Shugaba Omar Al-Bashir daga karagar mulkin kasar, kimanin shekara biyu da suka gabata.

Juyin mulkin na ranar Litinin dai na zuwa ne ’yan makonni gabanin shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula.