✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ka fito mu yi muhawara gaba-da-gaba idan ka isa —Atiku ga Tinubu

Muna kalubalantar Tinubu da ya fito gaba-da-gaba da Atiku domin nuna wa duniya cewar yana da masaniya da kuma cikakkiyar lafiya.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kalubalanci takwaransa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da ya fito su yi muhawara gaba-da-gaba ta tsawon sa’a daya kacal a gidan talabijin domin tattauna batutuwan da suka shafi kasar.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu wanda ya yi ikirarin cewa Atiku bai shirya mulkin kasar nan ba.

A bayan nan ne kwamitin yakin neman zaben ya mayar da martani ga kalaman da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi kan takarar musulmi da musulmi.

A wata hira ta musamman da ya yi da gidan talbijin na Arise TV ranar Juma’a, Atiku ya yi ikirarin cewa ya raba gari da tsohon gwamnan Jihar Legas ne saboda dagewarsa na zama abokin takararsa a zaben 2007.

A hirar tasa, Atiku ya ce takarar musulmi biyu a karkashin tikiti daya ne ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da Tinubu.

Dangane da hakan ne Atiku ya bukaci Tinubu da ya amsa gayyatar gudanar da mahawara a tsakanin su ta sa’a guda domin a bambance wanda ya cancanci jagorancin kasar a tsakaninsu.

Sanarwar da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya raba wa manema labarai ta ce, “muna kalubalantar Tinubu da ya gabatar da kansa domin gudanar da mahawarar awa guda da Atiku domin nuna wa duniya cewar yana da masaniya da kuma cikakkiyar lafiya kamar dan takarar na mu.

Ibe ya ce Atiku ya yi mamakin kalaman da ’yan amshin shatar Tinubu suka yi dangane da hirar da ya yi, musamman zargin cewar Atiku na gudanar da harkokin kasuwanci lokacin da yake aikin kwastam abinda ya saba wa doka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewar Atiku ya mallaki shaidar kammala karatun digiri na biyu a Jami’ar Anglia Ruskin sabanin sauran ‘yan takarar zaben shugaban kasar da ake da su a yanzu.

“Muna bukaci duk wani masi shaidar digiri irin wannan ko kasa da haka da ya gabatar domin jama’a su gani.”

Ibe ya kuma ce jama’a na iya bincike domin tabbatar da sahihancin shaidar karatun sa, amma kuma hakan ba mai yiwuwa bane ga wasu ‘yan takara.