✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka gaggauta magance yajin aikin ASUU da karancin mai – Kaigama ga Buhari

Ya ce jazaman ne shugabanni su rika sauraron koken jama’a.

Shugaban Darikar katolika na Abuja, Rabaren Ignatius Kaigama, ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kasance mai sauraren koken al’umma wajen gaggauta magance matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.

Da yake jawabi game da yajin aikin da malaman jami’o’i suka shiga da kuma karancin man fetur da ake fama da shi a kasar a halin yanzu, Rabaren Kaigama ya ce wajibi ne Shugaba Buhari ya gaggauta share wa mutanen Najeriya hawaye.

Ya ce jazaman ne shugabanni su rika sauraron koken jama’a, domin “Kasarmu ba za ta samu cigaba mai ma’ana da ake bukata ba, har sai idan ana sauraran juna cikin mutuntawa, tsakanin shugabanni da talakawa.

“Dole sai shugabannin gwamnati da na siyasa su kasance masu sauraron al’ummar kasa da mutanen da suke wakilta.

“Wannan ita ce hanya mafi inganci da za ta kawo cigaba da hadin kai da kwanciyar hankali a kasar nan.

“Uwa uba, za ta magance matsalolin da a halin yanzu suka yi mana katutu na karancin mai da kuma yajin aikin gargadi na tsawon wata guda da malaman jami’a suka shiga domin matsa wa gwamnati ta biya musu bukatunsu.”

Malamin addinin, ya ci gaba da cewa dole ne su kansu shugabanni su cire son rai su gyara halayyar su sannan su iya gyara wa mabiyansu kuskure, in kuma ba haka ba, tsuguno ba za ta kare ba.

“A yanayin da muke ciki yanzu, duhu ne ke bugun duhu tsakanin shugabanni da mabiya saboda mutanen da aka ba wa jagoranci ba su san girman nauyin da ya rataya a wuyansu ba, ballantana su yi aikinsu yadda ya kamata.

“Maimakon haka sun dauki mukamansu a matsayin wata dama ta yin rub-da-ciki a kan dukiyar jama’a, shi ya sa wasu har fada ko kisa za su iya yi domin su samu mukami,” kamar yadda ya bayyana.

Don haka ya yi kira ga shugabanni da cewa dole sai an kawo karshen yaudara da munafinci a harkar shugabanci, muddin ana so Najeriya ta kai ga tudun-mun-tsira.

A game da rikicin Rasha da Ukraine kuwa, Kaigama ya kuma isar da sakon Fafaroma Francis ga Kiristoci cewa su gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a ranar biyu ga watan Maris, 2022.