✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka maida hankali kan matsalolin Najeriya ba asalin Atiku ba —Timi Frank

Ya bukaci Malami ya mayar da hankali wajen warware matsalolin Najeriya ba neman asalin Atiku ba

Tsohon Mataimakin Sakataren jam’iyyar APC na Kasa, Timi Frank, ya yi raddi ga kalaman Ministan Shari’a, Abubakar Malami, game asalin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Malami ya bukaci wata kotun tarayya ta hana Atiku yin takara saboda ba dan asalin Najeriya ba ne.

Timi Frank, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce “Kamata ya yi ka maida hankali wajen warware matsalolin Najeriya ba neman asalin Atiku ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Atiku dan asalin Najeriya ne, wanda ya yi gwagwarmaya ciyar da dimokuradiyya da tattalin arzikinta gaba.

“Abun takaici ne fitowar wadannan soki-burutsu daga bakin mutum kamar Malami, musamman a wannan yanayi da kasa ke ciki.

“Irin wadannan kalamai ne suke haddasa rarrabuwar kai da fitina a tsakanin mutane.

“Ta yaya Malami zai ce Atiku ba dan Najeriya ba ne? Mutumin da ya taba yin takarar gwamna a Jihar Adamawa kuma ya ci, sannan ya yi Mataimakin Shugaban Kasa har na shekara takwas.

“Yaya za a yi a mutumin da ya taba aiki a Hukumar Hana Fasa Kauri ta Kasa, ya yi wa kasa hidima, a ce ba dan kasa ba ne?

“Wannan ba komai ba ne face wata siyasa wadda za a yi amfani da ita wajen bata sunan mutum mai nagarta kamar Atiku,” a cewar sa.