Ka ziyarci jihohin da ake kashe-kashe —PDP ga Buhari | Aminiya

Ka ziyarci jihohin da ake kashe-kashe —PDP ga Buhari

    Abubakar Muhammad Usman da Muideen Olaniyi

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da halin ko-in-kula da ta ce Gwamnatin APC ke nunawa kan hare-haren da ’yan ta’adda suke kaiwa a jihohin Sakkwato, Neja, Katsina, Kaduna, Filato da sauran sassan Najeriya suna kashe mutane da yawa.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sakataren PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce ya kamata Buhari ya ziyarci jihohin da abun ya shafa.

A cewarsa, yana da kyau Buhari ya kai ziyara jihohin don tabbatar da alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabensa na yakar ’yan ta’adda tare da nuna cewa shi kadai ne zai iya kawo karshen matsalar tsaro.

Sanarwar ta ce wannan ya nuna gazawar APC karara wajen samar da mafita a bangaren tsaro, wanda tabarbarewarsa ta kara tsanani a cikin shekara shida da suka gabata.

Ya ce “Abu mafi karanci da ’yan Najeriya ke sa rai shi ne gwamnatin APC ta samar da hanyar da za a kawo karshen matsalar tsaro, ta hanyar gano wadanda ke daukar nauyin masu aikatawa, kamar yadda gwamnatin ta sanar, amma ta gaza daukar matakin da ya dace.

“Sai dai APC ba ta da wani abun tabukawa face kawai son mulki.

“PDP tana jajanta wa wadanda munanan hare-haren ’yan bindiga suka shafa, kada su cire tsammani, amma su kasance masu taimakon juna ta hanyar sake gina kasar nan.”