✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kada a Dage Zaben 2023 —Rafsanjani

Kungiyar sanya iko kan ayyuka majalisun dokoki (CISLAC) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su daina batun yiwuwar dage babban zaben 2023,…

Kungiyar sanya iko kan ayyuka majalisun dokoki (CISLAC) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su daina batun yiwuwar dage babban zaben 2023, da kwanaki 44 da suka rage a gudanar da shi.

Babban daraktan kungiyar, Auwal Musa Rafsanjani ne ya bayyana cewa hakan zai jawo babbar matsala ga tattalin arzikin Najeriya.

“A ganinmu irin wadannan kalamai ba su da wani tasiri sai ma jawo barnatar da dukiyar al’umma, da cika wa makiya dimokradiyya burinsu na ganin ba a gudanar da babban zaben ba.

“A don haka muna ganin bai kamata a bari haka ta faru ba, kuma akwai bukatar bai wa jami’an tsaro da na hukumar zabe wadatattu kuma igantattun kayan aikin tunkarar kalubale irin wannan a lokutan zaben,” in ji Rafsanjani.