‘Kada karatun boko ya zama matsala ga aure’ | Aminiya

‘Kada karatun boko ya zama matsala ga aure’

 ta ba, wannan ba abu ne mai kyau ba, amma ka ga su kabilu suna da tsarin taimakon junansu ta fuskar aure. Don haka ina kira ga ’yan uwana mata bisa mahinmmancin sana’a, don ni ma shekaru sama da talatin a baya ba na sana’ar komai, sai dai maigida ya ajjiye mini masu taimaka mini aikin gida biyu ko uku ana biyansu, amma yanzu da na farga na fara sana’a na ga mahinmmancin ta, kuma mu daina takurawa mazajen mu a kan abin duniya,

 

A baya bayan nan kin samu sarauta na Gimbiyar Matan Shuwa Arab na Legas, da ma akwai ‘Yan Shuwa Arab da dama ne a Legas?

Haka ne mu ’yan Shuwa Arab muna da dama a Legas sannan muna da fitattun shugabanni a sassa daban daban kamar su Marigayi Grema Muhammad a Agege da Gaji Abubakar a Festak da su Sultan Jibrin Yaya Sarkin Shuwa Arab na Legas da kuma Shuwa Arab yan kasar Kamaru  da dai sauran makamantan haka, mu ma a matan muna nan da yawanmu da za mu samu goyon bayan shugabannin mu da za mu yi nasara wajan hada kan alummarmu, na kuma godewa maigidana da ya ba ni goyon baya a wannan sarauta na kuma samu goyon bayan ’yan uwana mata ina fatan Allah Ya taya ni riko Ya ba ni ikon samun damar taimakawa ’yan uwana mata da wannan mukami da muka samu.   Ina matukar godiya ga duk wanda ke da hannu a wannan lamari, kuma Alhamdulillahi yanzu mu matan Arewa a nan Legas muna da hadin kai inda muke da kungiyoyin taimakom kai da kai wadanda suka hada da sauran kabilu na Yarbawa da ’yan kabilar Ibo kuma muna samun cigaba daidai gwargwado.