✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kaduna 2023: Zan sauya wasu manufofin El-Rufa’i idan na ci zabe– Uba Sani

Uba Sani ya ce Gwamana El-Rufai mutum ne wanda bai kubuta daga yin kuskure ba.

Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce muddin aka zabe shi zai sauya tsare-tsaren da Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya shimfida wadanda ba su yi wa talakawan jihar dadi ba.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a wajen muhawarar da Sashen Hausa na BBC ya shirya wa ‘yan takarar Gwamna a Kaduna.

A cewar Uba Sani, “Zan tabbatar da duba wasu tsare-tsaren sannan in gyara marasa kyau daga ciki.

“Hakan zai kasance ne saboda gwamnan ya ce a matsayinsa na mutum, akwai yiwuwar samun kuskure a tsare-tsarensa wadanda za a gyara.

“Amma zan ci gaba da amfani da masu kyau daga ciki,” in ji Sani.

Ya kara da cewa, Gwamna El-Rufai mutum ne, don haka bai kubuta daga yin kuskure ba a wasu tsare-tsarensa, musamman a fannonin ilimi da bunkasa al’umma.

Su kuwa ‘yan takarar jam’iyyun NNPP da PDP, Sanata Suleiman Hunkuyi da Isa Ashiru, alwashi suka sha kan maido da malaman da aka kora daga aiki da rage kudin makaranta na jami’ar jihar
muddin suka lashe zabe.