✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaduna: An tsige Mataimakin Shugaban Majalisa

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta tsige mataimakin shugabanta, Hon. Muktar Isa Hazo sannan ta maye gurbinsa nan take. Zaman majalisar na ranar Alhamis 11 ga…

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta tsige mataimakin shugabanta, Hon. Muktar Isa Hazo sannan ta maye gurbinsa nan take.

Zaman majalisar na ranar Alhamis 11 ga Yuni, 2020, ya zabi Isaac Auta Zankai, mai wakilatar Kauru a matsayin mataimakin shugabanta.

Hon. Mukhtar Hazo ya rasa mukaminsa ne sakamakon zarginsa da yunkurin tsige Shugaban Majalisar, Hon. Yusuf Zailani.

Akawun Majalisar Bello Idris ya sanar da tsige Hon Mukhtar bayan 24 daga cikin ‘yan majalisar 34 sun  kada kuri’ar rashin nutsuwa da shi, sannan suka zabi Hon. Zankai ya maye gurbinsa.

Ya kara da cewa tuni sabon Mataimakin Shugaban Majalisar ya sha rantsuwar kama aiki.