✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin kujerun Hajji da aka ba jihohi a 2023

Kaduna ta samu kujeru 5,982, Kano kujeru 5,902, sannan Sakkwato 5,504.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NACHCON) ta ce jihohin Kaduna da Kano da Sakkwato ne suka samu kaso mafi yawa na kujerun aikin Hajjin bana.

Mataimakin Daraktan Yada Labaran NAHCON, Musa Ubandawaki, ya ce Jihar Kaduna ce kan gaba da kujeru 5,982, sai Kano mai kujeru alhazai 5,902, sannan Sakkwato, 5,504.

Sauran jihohin su ne:

  • Neja – 5,165
  • Katsina – 4,913
  • Kebbi – 4871
  • Kwara – 3,219
  • Legas – 3,576
  • Abuja – 3,520
  • Gombe – 2,301
  • Imo – Imo 30
  • Jigawa – 1,525
  • Filato – 1,984
  • Ribas – 50
  • Taraba – 1,590.
  • Abiya – 53
  • Adamawa – 2,669
  • Anambra – 39
  • Bauchi – 3,132
  • Bayelsa – 35
  • Binuwai – 236
  • Borno – 2,735
  • Kuros Riba – 66
  • Delta – 74
  • Nasarawa – 1,567
  • Ogun – 1,139
  • Ondo – 436
  • Osun – 1,054
  • Oyo – 1,441
  • Yobe – 1,968
  • Ebonyi – 117
  • Edo – 274
  • Ekiti – 197
  • Enugu – 40.

Sanarwar ta ce ba a kai ga fitar da adadin da aka ware wa jihar Kogi ba, har sai NAHCON ta kammala nazarin ayyukan hukumar a jihar.

Kazalika ta ce ba a bai wa jihar Akwa Ibom kujeru a bana ba, saboda rashin sabunta lasisinta na aikin Hajji.

“Ana sa ran dukkan jihohin kasar za su mika bayanan kashi 50 cikin 100 na kujerun kujerun 2022 da hukumar ta ware musu, kafin wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

“Rashin yin hakan daga kowace jiha, zai jawo mata ragin kujerun da za a ba ta a bana,” a cewar sanarwar.