✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafin ranar Asabar za a dawo da sadarwa a fadin Jihar Katsina —Masari

Masari ya jadadda cewa dole ne mutanen Katsina su kare kawunansu daga ’yan bindiga.

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce za a dawo da hanyoyin sadarwa a ragowar kananan hukumomin da aka datse kafin kamawar watan Janairun 2022.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai a Katsina a ranar Talata, inda ya jadadda cewa mutanen jihar su tashi tsaye wajen kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.

Idan ba a manta ba a baya gwamnatin Katsina ta bude hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 10 daga cikin 17 ta katse a fadin jihar saboda ayyukan ’yan bindiga.

Gwamnan ya kuma jinjina wa irin kokarin da ’yan banga ke yi a jihar wajen yaki da ’yan bindiga, sannan ya shawarci al’ummar yankunan da ’yan bindiga suka addaba da su tashi tsaye wajen kare kawunansu.

Ya kuma shawarce su da su kasance masu sanya ido da kuma taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace don kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Gwamnan, wanda ya ba da tabbacin a lokacin da yake sanya hannu kan kasafin kudin jihar na 2022, ya ce babu gudu, babu ja da baya a yakin da ake yi da ’yan bindiga a jihar.

A cewarsa, mutane sun san ’yan bindigar da ke zaune a tare da su, kuma dole ne a fallasa su domin su girbi abin da suka shuka.

“Dole ne mu shirya yakar su saboda sun kasance annoba a tare da mu.

“Mun karbi mulki a 2015 cikin matsalar tsaro kuma da yardar Ubangiji ba za mu sauka mu bar ’yan baya da wannan matsala ba. Dole ne mu dawo da abubuwa yadda suke.

“Mun karbi mulki da matsalar tsaro kuma dole mu kawo karshen matsalar kafin mika mulki ga wasu.

“Dole ne mu kare muhallanmu.

“Muna da abubuwa guda biyu; yawa da kuma fasahar zamani. Idan aka hada biyun waje daya komai zai iya dawowa daidai. Yin hakan ba zai fi karfinmu ba,” a cewar Masari.