✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafofin watsa labarai 52 da NBC ta soke lasisinsu

Gwamnati na bin tashoshin 52 bashin kusan Naira biliyan 2 da miliyan 600.

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai a Najeriya (NBC) ta soke lasisin tashoshin talabijin da na rediyo 52 daban-daban a sassan kasar.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon abin da hukumar ta kira gazawar kafofin watsa labaran wajen sabunta lasisin yada shirye-shiryensu.

A sanarwar da Shugaban NBC Balarabe Shehu Illelah ya fitar a ranar Juma’a, ya ce dukkanin tashoshin sun gaza biyan kudin sabunta lasisin inda gwamnati ke binsu bashi tun shekarar 2015.

A cewar Illelah, zuwa yanzu gwamnati na bin tashoshin 52 bashin kusan Naira biliyan 2 da miliyan 600.

Sanarwar ta kuma bayar da umarni ga ofisoshinta na jihohi da su hada gwiwa da jami’an tsaro wajen rufe kafofin watsa labaran da abin ya shafa a jihohinsu nan da awanni 24.

Illelah ya ce tun cikin watan Mayun da ya gabata, hukumar ta fitar da jerin sunayen tashoshin da ba su sabunta lasisinsu ba tare da ba su wa’adin makonni biyu su sabunta lasisin ko kuma a dauki matakin datse sadarwarsu.

Illelah ya ce watanni 3 bayan ba su wa’adin, tashoshin 52 sun gaza sabunta lasisin dalilin da ya sanya katse su a Juma’ar nan.

Ya ce soke lasisin yada shirye-shiryensu ya yi daidai da tanadin doka mai lamba CAPN11 karkashin sashe na 10(a) na Kundin Tsarin Mulkin na 2004.

Daga cikin kafofin watsa labaran da sokewar ta shafa sun hada da AIT, Silverbird, Rediyon Ray Power kana Greetings FM da Tao FM sannan Zuma FM da kuma Crowther FM da We FM baya ga Bomay Broadcasting Services.

Sauran sun kunshi MITV da Classic FM da Classic TV kana Beat FM da Splash FM da kuma Rock City FM da Family FM da kuma Space FM sannan Radio Jeremi.

Karin tashoshin da suka fuskanci wannan soke lasisi akwai FM Abuja da FM Lagos da FM Yenagoa da FM Port-Harcourt da FM Jos da kuma Wave FM da gidajen Rediyo mallakin jihohin Kogi da Kwara da kuma Neja.

Akwai kuma gidajen Radio na Benin Network da FM Network da FM Okene kana FM Suleja da FM Abuja da FM Benin da Breeze FM sai kuma Vibes FM da Family Love FM kana gidajen Radiyon Port-Harcourt da na Gombe da na Legas da Osun da kuma na Ogun da Ondo da Ribas da Bayelsa da Cross River da Imo da Anambra da Borno.

Sauran sun kunshi gidajen Rediyon jihohin Yobe da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Jigawa da Kaduna da Katsina.