✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka’idojin rubutun Hausa (3): Tarihin ka’idojin rubutun Hausa

A makon jiya mun ji yadda aka faro rubutun Hausa da bakaken Latin ko boko da wadanda suka fara amfani da shi da kuma littatttafai…

A makon jiya mun ji yadda aka faro rubutun Hausa da bakaken Latin ko boko da wadanda suka fara amfani da shi da kuma littatttafai na farko da aka rubuta da bakaken bokon.

To yau za mu dora daga kan yadda aka fara sanya ka’idojin rubutun daga nan sai mu tsunduma bayani kan wasu daga cikin ka’idojin.

Daga sunayen littattafan da muka gani a baya da yadda marubuta na farko suka rika rubuta sunayen abubuwa za mu fahimci cewa rubutun Hausar boko da aka fara wajen Karni na 18 da 19 ba su da wasu ka’idoji, wato rubutun ya gudana ne kara-zube ba wani tsari ko ka’ida da aka aza shi a kai.

Bilhasali ma marubutan suna yin rubutun ne gwargwadon yadda suka fahimci Kalmar da aka furta.

Misali yadda B.G. Niebuhr ya rubuta a littafinsa: “The life of Niebuhr” wanda aka buga a kasar Denmark a 1791:

Motum      –     Mutum

Koroma     –     Korama

Ghurassa   –     Gurasa

Berni         –     Birni

Daua          –    Dawa

Shinkaffer –     Shinkafa

Sirki          –     Sarki

Crua          –    Ruwa.

Hatta sunayen littattafan da Mista Schon J. F. Ya wallafa Hausar ba ta da fasali.

Misali yakan rubuta littafi ne da letafe alal misali; Letafen Magana Hausa da aka buga a birnin Berlin na Jamus a 1857, maimakon Littafin Maganar Hausa ko ma ya ce Littafin Hausa.

Haka ya rika rubuta letafe maimako littafi a sauran littattafansa da suka biyo baya kamar yadda muka gani a kashi na biyu da ya gabata.

  • Samuwar ka’idojin rubutun Hausa

To amma da yake Hausa ta yi gyadar dogo sai masana suka fara lalubo hanyar samar da ka’idojin rubutun Hausa don samar da daidaitacciyar Hausa da za a yi amfani da ita don ta shiga sahun sauran manyan harsunan duniya.

Abdullahi Garba Wurma: 2005, ya ce: “A shekarar 1912 aka kafa harsashe na daidaitacciyar (ko ka’idojin rubutun) Hausa a karkashin Dan Hausa (Hans Vischer) kuma an ci gaba da karfafa shi (harsashen) har zuwa 1988, lokacin da Hukumar Harshen Hausa ta tabbatar da shi.” (Daidaitacciyar Hausa da Ka’idojin Rubutunta; shafi na 2).

Sannan tun a 1933 aka fara tsara ka’idojin rubutun Hausa a karkashin Hukumar Talifi da aka kafa a wancan lokaci.

Kuma gwamnatin tsohuwar Jihar Arewa ta zamanin Turawan mulkin mallaka ta kafa Hukumar Harshen Hausa a 1955 don ta yi nazarin ka’idojin don yi musu gyare-gyare, inda daga nan ta sabunta ka’idojin.

  •  Samar da daidattaciyar Hausa:

Daga baya an ci gaba da gudanar da tarurruka kan hanyoyin inganta ka’idojin rubutun Hausa da samar da daidaitacciyar Hausa, inda aka yi irin wannan taro a 1966 a Bamako na kasar Mali.

Sai Jami’ar Ahmadu Bello ta kira wani taron a 1970, daga nan aka gudanar da wani taron da Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya ta Jami’ar Bayero ta shirya a 1972, duk dai don a samu matsaya kan

kalmomin harshen Hausa da za a rika amfani da su da kuma yadda za a rubuta su.

Taron na Jami’ar Bayero na 1972 ya yi nazarin ka’idojin da ake rubuta Hausa, aka sake sabunta wasu aka tace ka’idojin, aka jeranta su, aka rattaba su a wuri daya don daidaita su, su zama tsayayyun hanyoyin da duk mai nazari ko mai amfani da harshen Hausa a ko’ina a duniya zai rika amfani da su wajen rubutu.

  •  Bakaken Hausa:

Tunda mun ga yadda aka faro rubutu da Hausar boko da tarihin rubutun yanzu za mu fara darasi kan wannan batu.

Ga duk wanda zai rubuta wani abu dole ya san bakaken harshen da yake so ya yi rubutu a kansu.

Hausa tana da bakake iri biyu: gwaurayen bakake da masu goyo.

Gwauraye guda 19 da suka hada da:

Abdullahi Garba Ruma; (2005) ya ce: “Bakake suna cikin sautuka wadanda harsuna na duniya suke amfani da su a wajen magana.

Harafi (baki) yana nufin alamar da ke kwaikwayon muryar mutum a rubuce, kuma baki misali ne na harafi. A rubutun boko, wasali dole a Hausa.”

Sai ya fassara bakaken da cewa: “Su ne sautuka wadanda furucinsu ba ya faruwa sai an takura hanyar iska wadda take fitowa daga huhu.

A Hausa bakake iri biyu ne. Tilo ko gwauraye ko ki-jima da masu goyo.”

To a Hausa dai kamar yadda a bakaken Latin lamarin yake, muna da bakake da wasulla manya da kanana kamar haka:

  • Manyan bakake:

B V C D D F G H J K L M N R S T W Y Z

  • Kananan bakake:

b v c d d f g h j k l m n r s t w y z.

  • Masu goyo manyan bakake:

FY GW GY KW KW KY KY SH TS ’Y

  • Masu goyo kananan bakake:

fy gw gy kw kw ky ky sh ts ’y.

Jimillar bakaken Hausa sun zamo 29 ke nan. Sai wasulla guda biyar:

  • Manyan wasulla:

A I O U E.

  • Kananan wasulla:

a i o u e.

 

  • Nusarwa:

A lura akwai bakin da masana Hausa suke kira da alhamza da ka iya zuwa a farkon suna ko a cikin rubutu da ake rubuta shi da bakin ‘a’ kamar a suna Abubkar ko a bayani a ce ‘a kai kasuwa.’

In aka hada da shi kalmomin sun zama 30 ke nan.

Wadannan bakake da wasulla su ake hadawa a tayar da kalma, ma’ana a samu suna ko wakilin suna ko aiki ko wani harafi (baki) da zai taimaka wa ginuwar jumla a samu cikakkiyar magana.

Idan muka lura za mu ga cewa gwaurayen bakaken su ne wadanda suke zuwa a guda daya ko tilo inji Barebari, yayin da masu goyo suke zuwa su biyu daya goye a bayan daya.

Dukkansu sun samo wadannan sunaye ne bisa lura da yadda Bahaushe yake furta su a yayin magana, inda masana suka yi ittifakin hanyar da za a bambance wannan furuci shi ne yin goyo ga wadannan bakaken kamar yadda furucinsu yake nunawa.

  • Misalan gwaurayen bakake a cikin kalma:

Sun hada da: Baba, cillakowa, daddawa, dinki, fika, ganga, hula, jaki, kalangu, labi, magarya, namiji, rariya, sakata, tankade, wanka, yari, zanko da sauran misalai da za a iya kawowa.

Misalan bakake masu goyo a cikin kalma:

Sun hada da: Fyade, gwada, gyada, kyakkyawa, kyastu kwado, kwaro, shinkafa, tsamiya ’ya’ya da sauran misalai da za a iya kawowa.