✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kakakin Majalisar dokokin Taraba ya ajiye mukaminsa

Ya ce ya ajiye mukamin ne saboda dalilai na kashin kai

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Farfesa Joseph Aibasu Kunin, ya ajiye mukaminsa saboda dalilai na kashin kai.

Ajiye mukamin nasa na kunshe ne a cikin wata wasika da Mataimakinsa, Hammanadama Ibn-Abdullahi, ya karanta wa sauran ’yan majalisar a ranar Laraba, wanda kuma shi ne ya jagoranci zaman.

A cikin wasikar, wacce Aminiya ta sami ganin kwafinta, mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Disamban 2022, tsohon Kakakin ya ce, “Na rubuto domin na sanar da matakina na ajiye mukamina a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba.

“Ajiye aikin nawa na da nasaba ne da dalilai na kashin kai. Ina so na gode wa masu girma ’yan uwana ’yan majalisa saboda hadin kai da goyon bayan da suka ba ni, lokacin da nake kan kujerar.”

Sai dai Aminiya ta gano cewa majalisar ta zabi sabon Shugaban bayan ajiye aikin tsohon Kakakin.

A yayin wani zaman gaggawa, majalisar ta zabi John Kizito Bonzena a matsayin sabon Kakakin da murya daya.

Kafin nadin nasa, John dai shi ne Bulaliyar majalisa kuma shi ne yake wakiltar mazabar Zing ta Jihar.