Kalubalen da ke gaban Jam’iyyar APC gabanin babban taronta | Aminiya

Kalubalen da ke gaban Jam’iyyar APC gabanin babban taronta

    Muhammad Aminu Ahmad da Adam Umar

A ranar Asabar 26 ga wannan wata, ake sa ran Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da babban taronta na zabar sabbin shugabanni da za a danka wa ragamar tafiyar da jagorancin jam’iyyar.

Mutum takwas ne ke takarar shugabancin jam’iyyar, duk kuwa da rahotannin da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayan wani daga cikin su.

Masana dai na cewa babban taron yana da tasiri sosai a kan makomar jam`iyyar ta APC.

Wannan shi ne karo na farko da jam’iyyar ke zaban shugabannin, kasancewar dukkan jagorori uku da su ka shugabanci jam’iyyar a baya, wato CIf John Oyegun da Cif Adams Oshiomhole da kuma Gwamna Mai Mala Buni da ke a yanzu, sun hau mukamin ne ba tare da yin zabe ba, kamar yadda mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum kuma masanin shari’a Barista Mainasara Kogo Umar, ya shaidawa Aminiya.

Duk da cewa shugaban riko na Jam’iyyar APC, gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni da ’yan kwamitinsa sun bayyana cewa shiri ya yi nisa game da babban taron jam’iyyar na kasa da ake sa ran gudanarwa a goben, a bangaren masu neman takara za a iya cewa tana kasa tana dabo ganin cewa mutum takwas ne ke neman shugabancin jam’iyyar.

Bakwai daga cikin su, Malam Saliu Mustapha da Malam Mohammed Etsu da Sanata Mohammed Sani Musa da Sanata Tanko Al-Makura da Sanata George Akume da Sanata Abdullahi Adamu duka sun fito ne daga shiyyar Arewa ta tsakiya.

Sai na takwas, shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar Arewa maso Yamma.

Ko da yake akwai Sanata Ali Modu Shariff, da ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabas, wanda ya ce ya janye daga takarar saboda rahotanni na cewa akwai wani shiri da ake yi don daidaitawa a bar kujerar ga wani dan takara, kuma a cewarsa Shugaba Buhari na goyon bayan shirin maslaha ko daidaitawar.

A cewar Sanata Ali Modu Sheriff, “Shugaban kasa na son shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa ta Tsakiya. Shugabanmu ne, babanmu ne, duk abin da yake so shi za mu yi. Ni ba na jayayya da iyayena a kowane fanni,” in ji shi.

Sai dai Barista Mainasara ya ce jam’iyyar ta gaza wajen samawa kanta ’yan kwamitin amintattu da ke matsayin masu tsawatarwa idan a ka fuskanci akasi.

Ya ce hakan ya sa an zubawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ido a matsayin wanda zai cike wannan gibin, sai dai ya ce kusan sa ido kawai shugaban kasan ya rika yi a tsawon lokacin, a yayin da a wani zubin kuma tsawatawar tasa ke zuwa a makare a matsayin ta fargar-jaji, inji shi.

Tuni daukacin ’yan takaran shugabancin jam’iyyar su bakwai su ka mika takardar neman tsayawarsu ga ofishin jam’iyyar da su ka cika bayan kowannensu ya saya ko an saya masa a kan kudi Naira miliyan 20.

Dan takara na takwas da ya janye takararsa bayan cika fam din amma ba tare da mayarwa ba, shi ne tsohon gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sherif.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci babbar sakatariyar jamiyyar a ranar Talata kwana 3 gabanin taron, ya samu labarin cewa a ranar ce a ka fara tantance masu neman tsayawa mukaman jam’iyyar inda a ke tantance takardun shiadar jam’iyya da kuma mallakar katin zaben na dan takaran da takardar kammala makarantar sakandare, da kuma duba yankin da a ka baiwa kujerar, sai kuma tallafin dan kara ga jam’iyyar.

Wani jami’in jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce sai dai sabanin yadda a ke saran gudanar da taron a babban ofishin, an kai shi ne zuwa masaukin gwamnan Jihar Katsina da ke Abuja wato Alhaji Aminu Bello Masari, wanda ke matsayin shugaban kwamitin gudanar da taron.

Baya ga takarar kujeran shugabancin jam’iyyar na kasa, akwai kuma na mataimakansu na shiyyar yankunan Arewa da kuma Kudu.

A yayin da jam’iyyar ta amince da bada takarar kujeran mataimakinta na Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa na yankin Arewa ga shiyyar jihohin Arewa maso Gabas, ta kuma ware kujeran mataimakinsa na Kudu ne ga jihohin shiyyar Kudo maso Gabas, kamar yadda ta ware na sakataren jam’iyyar na kasa ga shiyyar ta Kudu maso Gabas. Akwai kuma wasu tarin mukaman da za a yi takararsu a zaben na goben.

Gabanin zuwan ranar zaben hankali ya koma kan samar da ’yan takara na hadin gwiwa da nufin rage zafin hamayya a zaben, inda gwamnoni ke kokarin kasafta mukaman a tsakanin wadanda su ke son marawa baya.

Duk da cewa ba a kai ga matsaya ba a kan wanda masu fada a ji na jam’iyyar ke son marawa baya ba, a matakin shugabancin jam’iyyar, akwai hasashen cewa za a yi karon batta ne a tsakanin ’yan takara biyu wato sanata Abdullahi Adamu da kuma Sanata Umaru Tanko Al-makura, inda wasu majiya ke nuna cewa Sanata Abdullahi Adamu na da goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahotanni dai na cewa jiga-jigan APC a shiyyar Arewa ta tsakiya, musamman ma gwamnoni da kuma Sanatoci daga bangarorin Najeriya daban-daban sun dukufa suna ta tuntuba don cimma maslaha ta yadda za a daidaita a kan mukamin shugaban jam`iyya da sauran mukamai.

Amma wasu rahotannin na cewa ana fuskantar turjiya.

Alal misali, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ce maganar maslaha ba za ta hana shi jarraba irin nasa farin jinin ba.

Alhaji Ibrahim dan Malikin Gidan Goga na cikin na hannun daman tsohon gwamnan kuma ya bayyana cewa “yana cikin wannan takara amma abin da muka sani shi ne an ce an kebe kujerar Shugaban kasa ta koma Kudu, kujerar shugaban jam’iyya ta dawo Arewa.Wata Magana wai a kebewa wani yanki mu duk ba mu san wannan ba”.

Sai dai inda za a fuskanci kalubale shi ne barazanar da ake ganin bangaren Abdulaziz Yari nayi na cewa za su iya ficewa daga jam’iyyar idan ba a yi mu su adalci ba.

Su ma masana kimiyyar siyasa na ganin cewa Jam`iyyar APC za ta iya lallaba `ya`yanta su yi babban taro. Sai dai bayan taron ne wasu daga cikin `ya`yan nata za su nuna akalarsu.

Farfesa Husseini Tukur malami ne a jami’ar Jihar Nasarawa, kuma ya ce “kowa yana kokari ne ya samu abin da yake bukata, a halin yanzu akwai ‘yan takara da dama, akwai wadanda suka fito daga tsakiyyar Najeriya da Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yamma. Wannan yana nuna cewa wajibi ne tun da tsarin mulkinsu bai nuna za a ware mukamin ba, toh a ba kowa dama ya yi takara”.

Masanin ya ce a bayanne take cewa jam’iyyar tana cikin rudani saboda akwai bangarori da dama a cikinta.

Sai dai shugabannin Jam`iyyar APC sukan ce duk jam`iyyar da ta cika ta batse ta gaji hayaniya, ballantana APC mai mulkin kasa kuma suna daukar matakan daidaita kan `ya`yan jam`iyyar ta yadda za su samu mafita ga kowane irin rintsin da za su shiga.

Da ya kara tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, Barista Mainasara Kogo Umar, ya ce ’yan majalisar dokoki na tarayya sun yi kokari wajen tsabtace lamarin zaben tare da rage karfin kane-kane da gwamnoni ke yi kan zaban shugabannin jam’iyya da kuma na fidda gwanin a ‘yan takara sauran zabuka na gama gari.

Sai dai a cewarsa lamarin ya samu koma baya, bayan wata kotu ta yi hukuncin kan soke dokar kamar yadda ya ce Ministan shari’a Abubakar Malami ya dade ya na yunkurin ganin dokar bata kai labari ba tun a farko.

Shima wani tsohon dan Jam’iyyar APC da a yanzu ya koma Jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Khalid Isma’il, cewa yayi Jam’iyyar APC na da tarin matsaloli da kararraki a kanta da ya dara 200, ya ce jam’iyyar ta gaza samun nasara a zabukanta na wasu jihohi, inda ya ce ya na da wuya ta samu nasara a mataki na kasa.

Sai dai a lokacin da wakilinmu ya tuntubi Daraktan sashin yada labarai na jam’iyyar Malam Salisu Na-Inna, Daraktan ya ce komi na tafiya dai-dai kamar yadda a ka tsara, inda ya tabbatar da cewa tuni a ka fara tantance ’yan takaran tun a ranar Talatar data gabata.

Wasu da Aminiya ta zanta da su a kan lamarin, sun ce tarin matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta bai rasa nasaba da hadakar gamin gambiza da ya kawo jam’iyyar a matsayin dunkulalliya da wasu suka fassara da tsintisiya mara madauri.

Gabanin zaben shekara ta 2015 da ya kai jam’iyyar ga nasara jam’iyyu biyar ne suka hadu suka narke, da suka hada da CPC da ACN da ANPP da sabuwar PDP, sai kuma bangare na Jam’iyyar APGA.

Wasu na ganin cewa babban burinsu shi ne na kwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki a lokacin, PDP sannan bayan samun mulkin sai jagororin tsoffin jam’iyyun suka fara samun sabani a kan yadda za a kasafta madafun iko.