✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalubalen da ke gaban malaman addini a Arewa

Matsaloli sun dabaibaiye mu, amma hankalin malamai da mabiya ya yi wani wurin.

Wani abu da na lura da shi wanda ya kamata malamanmu na addini da mabiya a Arewacin Najeriya su duba su kuma gyara shi ne yadda dukkansu suka shagaltu da rikicin akida ko kawo rudani ko yi wa juna yarfe da miyagun maganganu na aibata wasu da suka aikata wani laifi.

Na farko maganar cusa wa mabiya zazzafar akida da gabar bangaranci ba su ya kamata mu mayar da hankali a kai ba, musamman a wannan lokaci.

Ina ganin kamata ya yi mu ba da muhimmanci ga al’amarin Da’awa da koya wa mutane shika-shikan addini da ibada da kyawawan halaye na mu’amala da kyautatawa da nuna kauna da yafiya — hakan zai taimaka wajen rage yaduwar munanan ayyuka.

– An bar jaki ana dukan taiki

Wani abin mamaki da ya kamata mu duba shi ne, har yanzu a cikin manyan garuruwan Hausa da muke da su fa akwai maguzawa da ba su da addini.

Babban misali shi ne jihohin Kano da Katsina suna da wani adadi mai girma na maguzawa wadanda ’yan asalin jihohin ne, baya ga Fulani wadanda ba su da ilimin addini sai kiwon shanu.

Amma har yanzu ba wata kungiya da take bin wadannan maguzawa domin ta yi musu wa’azi don ganin ta jawo hankalinsu sun shiga addini.

Maimakon haka, kullum daga rikicin akida sai yayata laifin shugabanni — ban sani ba neman suna ne yake jawo hakan ko kuma kokarin gyara ne da gaske.

Amma a zahiri an ki ba wa abin da ya dace muhimmanci, sai wanda ba shi ne ya fi damun talakan kasar nan ba.

Na samu bidiyon wata Bafulatana mai shekara 20 daga wata ruga a Karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa, wadda ta ce a rugarsu akwai mutum sama da 200, amma ba a taba samun wani malami da ya je don koya musu addini ba.

Mutum zai iya tunanin duk ’yan garin ma haka suke. Ba fa a maganar yadda suke sallah ballantana wankan tsarki ko auratayya a irin wadannan rugage da ake da su da yawa a Arewacin kasar nan.

Amma sai ga shi malamanmu sun bige da rikicin akida, har su hau kan mimbari suna zagin ’yar fim Rahama Sadau, suna fada wa mabiyansu cewa binciken da ake yi a kan DCP Abba Kyari fada ne da Musulunci, ko su ce rashin aminta da salon mulkin Buhari fada da addini ne, da sauran abubuwa marasa amfani.

– Maganganun siyasa

Na biyu, abin da malamanmu da yawancin mutanenmu suka fi sakawa a gaba kamar tsokaci a kan sha’anin siyasa da kuma gasar kara aure da tara mata ko yada laifin wasu ko caccakar su da sunan martani.

Mutanenmu sun mayar da hankali wajen aibata masu aikata laifi maimakon kiran su zuwa ga shiriya.

Sun manta cewa Allah Yana yafe wa duk wanda ya tuba gare Shi, sannan aikata laifi daya bai isa ba ya zama hujja cewa wanda ya aikata wannan laifin ya tabe har abada.

– Mu dawo cikin hankalinmu

Abu na uku, a maimakon mu mayar hankalinmu a kan manyan matsalolin da suke damun mu, suke ta rusa yankinmu, mun koma sai surutai barkatai a kan kananan abubuwa marasa muhimmanci a rayuwarmu da ci gaban kasarmu; kusan a kullum sai an yada sakon da ke iya raba kan al’umma.

Ina ganin ya fi dacewa mu karkatar da tunaninmu zuwa ga wayar da kan al’ummarmu a game da matsalolin da suka dangance su, kamar matsalolin yawan haihuwa da aure-aure barkatai, wadanda suke daga cikin abubuwan da ke kara haifar da rashin tsaro a yankin Arewa.

Dalili shi ne yadda rashin kula da ’ya’ya yake kawo tabarbarewar tarbiyya da karuwar kananan yara da ke yawo a titi babu karatu, babu ayyukan yi, saboda iyayensu sun  watsar da su. Wasu yaran kuma bata-gari suke amfani da su don ta da hankali.

Sauran matsaloilin sun hada da yawan mabarata a titi, ga rashin kyakkyawar mu’amala, sai ganin kyashi da hassada da bakin hali, wadanda duk ba koyarwar addini ba ne.

– Kafirta juna

Amma abin takaici malamanmu a majalisinsu, sun fi so su rika karantar  da cusa abin da zai kawo gaba da kiyayya, alhali mutane ko wankan gawa ba su koya wa mutane ba, ballantana yadda ake zamantakewar aure, ko hakkin mata da ’ya’ya a kan magidanta.

Kullum sai dai wannan ya kira wancan mushiriki, wancan ya kira wannan makiyin Annabi.

Malamai suna take gaskiya da yin shiru a kan halin kuncin rayuwa da talakawa suke ciki, saboda addininmu daya da masu rike da mukaman siyasa.

– Fuskantar gaskiya

Gaskiya ba zai yiwu mu ci gaba da rayuwa a haka ba, ya kamata mu rika yin addinin nan kamar yadda ya zo mana, ba wai da ra’ayinmu ba.

Mu fuskanci matsalolin da suke damun mu, mu magance su tun da wuri, mu ajiye son zuciya da neman tara mabiya ko wani abin duniya.

A yanzu ba wani yanki da ya kai shiyyar Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas tarin ’yan ta’adda masu dauke da muggan makamai, marasa imani wadanda yawancinsu Hausa/Fulani ne.

Sun mayar da satar mutane da yin garkuwa da su don karbar kudin fansa sana’a — suna kai hare-hare suna satar dukiyar jama’a.

Suna zaune babu ilimin addini, ba su san darajar dan-Adam ba, sai shaye-shaye da daukar makami.

Ni dai ban ga wani kokari da ake yi na neman a gano abin da ya sa wasu mutane daga cikin al’ummar Hausawa da Fulani suka shiga harkar ta da zaune tsaye ba, ko suka zama ’yan ta’adda.

Ta yaya Boko Haram da ISWAP suke samun yara kanana da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci?

Me zai hana mu tsayar da tunaninmu wajen nemo wa kanmu mafita a Arewa?

Yaya za mu yi nazarin tarihinmu da al’adunmu don samar da sauyin da muke son gani a yau?

– Har yanzu malamai na da kima

Har yanzu ana ganin mutuncin malamai har mabiya na kokarin aikata abin da suka fada musu, gwamnati kuma ba a ganin mutuncinta sosai, su ma sarakuna darajarsu ta zube.

Saboda haka malamai su ne suka rage da za su dage wajen kawo gyara a cikin wannan al’umma, amma fa sai sun cire son zuciya da neman abin duniya, su yi don Allah, sannan su tunkari ainihin matsalolinmu.

Idan kuma suka bari wannan damar ta kubuce musu, aka daina ganin su da kima da martaba to, sai dai kuma abin da hali ya yi.

– Lokaci mafi dacewa

Ni dai har a zuciyata, wannan shi ne lokaci mafi tsananin kunci da na tsinci kaina a ciki, a matsayina na Musulmi kuma Bahaushe, saboda yawancin abubuwan da nake gani ana yi, da kuma inda muka fuskanta ba hanya ce ta ci gabanmu ba.

Ya kamata mu fara tunanin mafita, ba malamanmu kadai ba, har da mabiya.

Wanme kokari muke yi wajen ganin mun gyara matsalolin da yankinmu da mu kanmu muke fama da su?

Abdul Abdul, ya rubuto wannan makala ne daga Jos; [email protected]