✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamaru ta kare martabar matsayi na uku a gasar AFCON

Burkina Faso ce ta fara zura kwallaye uku cikin mintina 49 amma a karshe reshe ya juye da mujiya.

Kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta lashe matsayi na uku na gasar a ranar Asabar.

’Yan wasan Indomitable Lions sun lallasa takwarorinsu na Burkina Faso da ci 5-3 a bugun fenareti bayan da aka tashi da ci 3-3.

Wani abin mamaki a wasan shi ne Burkina Faso ce ta fara zura kwallaye uku a ragar Kamaru cikin mintina 49 amma a karshe reshe ya juye da mujiya.

Kamaru ta yi kukan kura inda ta samu nasarar farke duk kwallaye ukun, lamarin da ya kai wasan ga bugun fenareti bayan da aka tashi da ci 3-3.

Kamaru dai ta kare a wasan neman matsayi na uku ne bayan da ta sha kaye a hannun Masar bayan bugun fenareti.

Hakan ya ba Masar din damar zuwa wasan karshe tare da Senegal.

Ita kuma Senegal ta kai wasan karshe ne bayan da ta doke ’yan wasan Burkina Faso da ci 3-1.