✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamata ya yi a mayar da Hausa yaren Kasa a Najeriya – Farfesa Dangambo

“Hausa na da saukin koyo, zai iya daukar kowanne nau’in ilimi komai zurfinsa.”

Wani Shehin Malami a bangaren Adabin Hausa, kuma malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Abdulkadir Dangambo ya ce karan harshen Hausa ya kai tsaikon da za a mayar da shi yaren kasa a Najeriya.

Farfesan, wanda ya shafe shekaru masu yawa yana koyar da harshen na Hausa a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da Aminiya a kan bikin ranar Hausa na bana.

Ana gudanar da bikin ne a kowacce ranar 26 ga watan Agusta domin yin waiwaye a kan muhimmancin yaren da kuma duba hanyoyin ciyar da shi gaba.

A cewarsa, “Alamu na nuna kamar akwai gasa tsakanin manyan harsunan Najeriya guda uku na Hausa da Ibo da kuma Yarbanci.

“Amma harshen Hausa na dada yin suna a duniya, kuma ko a Najeriyar ma ya fi dukkan sauran yawan masu amfani da shi.

“Ina ganin yaren karansa ya kai tsaikon da za a iya amfani da shi a matsayin yaren kasa saboda yana da saukin koyo, kuma zai iya daukar kowanne irin nau’i na ilimi, komai zurfinsa.

“Za ka iya amfani da Hausa wajen koyon hatta darussa masu wahala irin na kimiyya da fasaha (ciki har da na fasahar Nukiliya), kuma za ka iya bayyana duk abin da ka ke so a cikinsa cikin sauki,” inji Farfesa Dangambo.

Malamin jami’ar ya kuma ba da shawarar a rika koyar da yara ’yan makaranta da yaren na Hausa a matakin Firamare, yayin da daga bisani za a iya fara koya musu sauran yaruka in suka kai matakin Sakandire.

Ya yi bayanin cewa matukar Najeriya ba ta rungumi daya daga cikin yarukanta a matsayin wanda za a rika amfani da shi a matsayin na kasa ba, babu inda zata je a bangaren ci gaba.