✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Coca-Cola ya maka Pop-Cola a gaban kotu

Kamfanin Coca-Cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages da ke sarrafa lemon Pop-Cola a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano bisa zarginsa da satar…

Kamfanin Coca-Cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages da ke sarrafa lemon Pop-Cola a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano bisa zarginsa da satar fasahar alamominsu.

A cikin watan Yunin 2021 ne dai aka kaddamar da lemon na Pop-Cola, kuma tun a lokacin yake ci gaba da samun karbuwa a Kano, wacce cibiyar hada-hadar kasuwanci ce a Najeriya.

A cikin karar dai, Coca-Cola na zargin kamfanin na Mamuda da yin amfani da alamar da ta yi shige da irin tasu, tare da zuba lumukan a cikin mazubai da launin da zai rikitar da masu saye su kasa banbance su.

Masu karar dai na neman kotun da ta haramta wa wadanda suke kara daga ci gaba da yin amfani da alamar a jikin kowanne lemon nasu, motocin sufurinsu, allunan tallace-tallace ko kuma yin amfani da shi ta kowacce fuska ta kasuwanci, har zuwa lokacin da za ta kai ga yanke hukunci na karshe.

Kamfanin na Coca-Cola ya kuma ce daga cikin dalilan da ya sa yake neman kotun ta dauki matakin akwai yadda biliyoyin kwastomominsu a fadin duniya da suka jima suna amfani da kayayyakinsu da kuma yadda suka kashe makudan kudade tsawon lokaci wajen tallace-tallace da kuma daukar nauyin gasa iri-iri a kafafen yada labarai daban-daban.

A kan haka ne Coca-Cola ke zargin kamfanin na Pop-Cola da zama cima zaune ta hanyar satar fasahar da ya shafe tsawon shekaru yana ginawa.

Sai dai alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 11 ga watan Disamba mai zuwa.