✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Google zai sallami ma’aikatansa 12,000 daga aiki

Hakan na nufin kamfanin zai sallami kaso 6 cikin 100 na ma'aikatansa a fadin duniya

Kamfanin Alphabet, wanda ya mallaki shafin Google a ranar Juma’a ya sanar da cewa zai sallami mutum 12,000 daga cikin ma’aikatansa da ke fadin duniya saboda matsin tattalin arziki.

Hakan dai ya sa kamfanin ya bi sahun takwarorinsa manyan kamfanonin sadarwa da ke Amurka da suka sanar da yin sabbin sauye-sauye a cikinsu.

Kazalika, sanarwar ta Google na zuwa ne kwana daya baya kamfanin Microsoft shi ma ya sanar da shirinsa na sallamar ma’aikata 10,000 a watanni masu zuwa, yayin da kamfanin Meta wanda ya mallaki Facebook da kuma kamfanonin Amazon da Twitter su ma suka sanar da irin wadannan matakan.

Lokacin da ake tsaka da fama da dokar kulle sanadin annobar COVID-19 ne dai kamfanonin suka yi ta dibar ma’aikata ba ji ba gani don su iya biyan bukatar yawan mutane da ke tururuwar amfani da shafukansu saboda ayyuka, karatu da kuma harkokin nishadi.

A wani sako da ya aike wa ma’aikatansa ta imel, Shugaban kamfanin na Google, Sundar Pichai, ya ce, “A tsawon shekaru biyun da suka gabata, kamfaninmu ya bunkasa sosai.

“Domin mu iya biyan bukatar dimbin masu hulda da mu, mun debi mutane da dama aiki, amma yanayin tattalin arzikin da muke ciki a yanzu ya bambanta da na wancan lokacin,” in ji shi.

Sundar ya kuma ce za su yi kwaskwarimar ce domin su tabbatar iya wadanda ake bukatar ayyukansu a yanzu ne kawai suke cikin lalitar kamfanin, inda ya ce za a rage yawansu da mutum 12,000.

Ya zuwa karshen watan Satumbar bara, Kamfanin dai na da ma’aikata kimanin 187,000 a fadin duniya.

Rage yawan ma’aikatan da wancan adadin dai na nufin Google zai sallami kaso shida cikin 100 na ma’aikatan nasa, kuma korar za ta shafi sassa daban-daban ne kuma daga bangarori daban-daban na duniya.